Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027, kuma tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan naɗin wasu mutum biyu ’yan kabilar Yarabawa a muƙaman gudanarwa masu muhimmanci a Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).
Mutanen da aka naɗa su ne Mrs Oluyemi Titilayo Adeyemi-Showunmi, wadda za ta jagoranci sashen gudanar da zaɓe da rajistar masu kaɗa ƙuri’a, da Dr Lawrence Bayode, wanda aka naɗa shugaban sashen fasahar sadarwa ta zamani (ICT).
Atiku ya ce naɗin mutanen da ya bayyana a matsayin ’yan kabilar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kwanaki kaɗan kafin zaɓen shugaban ƙasa, abin damuwa ne da ya kamata a duba sosai.
Sai dai wannan damuwa ta fito ne daga Atiku, kuma ba ta zama hujjar cewa waɗanda aka naɗa ba za su gudanar da aikinsu cikin adalci ba.
— MIKIYA






