Home Daga Marubutanmu RAUNIN RAYUWA: Fita Ta Ɗaya

RAUNIN RAYUWA: Fita Ta Ɗaya

31
0

RAUNIN RAYUWA 

Na

Rukayya Ibrahim Lawal (Ummu Inteesar)

AREWA WRITERS ASSOCIATION 

Godiya; Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga ubangijina makaɗaici wanda ya ƙaga halittata ya azurta ni da baiwa da hikimar shirya saƙona a bayanance ta yadda zan isar da saƙona a fayyace, ga masu gani har ma da waɗanda suke a kurumce, saƙon ya zaga ko’ina ya yi bayanin rayuwarmu a al’adance.

Tsira da aminci su ƙara tabbata ga fiyayyen halitta annabin ƙarshe kuma shugaban manzanni ubangiji ka yi aminci ga iyalan gidansa da sahabbansa da waɗanda suka maye musu bisa koyarwarsa har zuwa kanmu.

Gargaɗi; Wannan labarin ayananne ne ban rubuta don cin zarafin wani ko wata ba, idan ka ga abin da ya yi kama da rayuwarka to arashi aka samu, haka nan ban yarda a yi amfani da labarin ba ta kowacce siga ba tare da amincewata ba.

Sadaukarwa: Na sadaukar da wannan shafin ga ƙungiyata mai albarka wato Arewa writers Association tafiyar aminci, tafiya mai cike da mutunta juna. Jama’armu na ciki da wajen ƙungiya masu yi mana fatan alheri don so fisabilillahi.

Gaisuwa: Ina miƙa saƙon gaisuwata ga babbar anti Hauwa S Zaria shugabar ƙungiyarmu da Fatima Sunusi Rabi’u Aminiyas tare da Lubabatu Auta Ingawa dukkaninku ba na yar wa domin kun taka rawar ganin wurin ganin nasara ta ta ɗore. Ubangiji ya jiɓanci lamurranku da na iyalanku.

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

 Page 1

Juye-juye take a uwar ɗakanta ita kaɗai kamar za ta mutu, sai cije leɓe take idonta na shatatar da hawaye laɓɓanta na rawar disco, tsananin azabar ciwon marar da take fama da shi a yau tun safe ya ba ta tabbacin naƙuda ce ta taso duk da kuwa ba ta taɓa haihuwa ba. Ba za ta iya ko da matsawa daga inda take ba ballantana ta kira wani mai taimako, ga shi ba kowa a gidan sai ita kaɗai. 

Mijinta tun safe da ya ba ta magani ya tsallake ya fita bai waiwayo ba, ba kuma waya a hannunta don haka ta yanke hukuncin taimakon kanta da kanta ta hanyar yin duk wata addu’a da ta zo bakinta. Cikin ikon Allah ta fara jin alamun sauƙi, ta fara hutawa na mintinan da ba su fi goma ba sai ga abar ta sake gangamo kayanta gadan-gadan, wannan lokacin ba ta ja tsawon lokaci ba Allah ya taimake ta abin ya faɗo. 

Ajiyar zuciya mai ƙarfi ta sauke tana sharce gumin fuskarta tare da ambaton sunan Allah. Sannu a hankali ta ɗaga dubanta zuwa inda abin da ta haifa yake kwance cikin jini, mamaki da tsoro suka shige ta. ‘Da ma a haka ake haifar yaro ko nata ne ya zo da wannan siffar?’

Kawar da zancen zucin ta yi ta hanyar yunƙurawa da dabara ta tallabo shi ta nannaɗe cikin zanin da ke gefenta ta rungume shi tare da jan ciki zuwa ga ma’adanar da ke kusa, ta yi sa’ar ganin reza sai dai ba sabuwa ba ce ta yi amfani da ita sau ɗaya. Bayan yin nazari na ‘yan sakanni ta tuna yadda ta ji labarin ake yanke cibi, don haka ta kwatanta iya abin da take tunanin daidai ne ta yanke. A wurin ta yadda rezar ta kuma kwanciya cikin jinin da ya ɓata gun ta ƙanƙame ɗan tayin a ƙirjinta.

Bayan mintuna 15 ta miƙe cike da ƙarfin hali ta kalli halittar da ta haifa, a jinsi dai namiji ne saboda ta gano shi da siffar kaɗangare sai dai ya yi ƙanƙanta da yawa.

 Duk da ba ta da cikakken sani game da rayuwa da yadda ake gane salwantar ta amma ta ji a ranta abin da ta haifa ba ya raye, don ba ta ga alamar numfashi ko motsi a tattare da shi ba, ballantana a je ga batun kukan jira-jirai na farko a duniya Kodayake ma ai bai isa haihuwa ba ƙaddara ce ta janyo faɗowarsa.

 A nan ta miƙe riƙe da shi ba tare da dogon nazari ba ta dafa bango zuwa banɗaki ta buɗe shadda ta jefa ɗan tayin a ciki tare da danna makunnar ruwan, nan da nan ɗan ya bi ruwan ya yi cikin rami.

Hawaye masu zafi suka ci gaba da zubo mata. Ita a iya tunaninta ba ta hango wani abin da ya cancanta da shi ba face haka tun da dai ko an ajiye shi ba zai yi amfani ba. Komawa gun ta yi ta kishingiɗa ta ƙara hutawa na ɗan dogon lokaci sannan ta sake tashi ta ƙarfafa jikinta ta tsaftace gun da ta ɓata a galabaice, ta ɗora ruwan zafi ta gyara jikinta ta koma ta kwanta tana mayar da numfashi. Iya ita kaɗai sai ubangijinta ne suka san irin zillar ciwon da take ji.

Can bayan azahar sai ga shi ya shigo gidan, bai damu da yin sallama tun a ƙofa ba sai da ya zo tsakiyar falon sa’annan ya yi sallamar da iya kansa kawai ya jiyar sai wani haɗe fuska yake yi.

Da ya ƙare dube-dubensa ya tabbatar ba ta falon ne ya kutsa kai zuwa uwar ɗaka ya hango ta kwance a kan gado ta ba wa ƙofar baya.

 “Ke! Wannan wane irin lalaci ne za ki bar gidan a hargitse ki zo nan ki kwanta? Kuma shi ne ina sallama ma ba za ki iya amsawa ba tsabar kin raina ni?”

Ita kam a lokacin har wani baccin ni’ima ya fara ɗibar ta ta ji saukar dundu a gadon baya tun da ta yi wata ƙara sau ɗaya ba ta iya ƙara yin komai ba, numfashinta ne ya sarƙafe na wucin gadi kafin ya dawo ta ci gaba da sauke ajiyar zuciya. Har ya ɗaga hannu da nufin ƙara kai mata wani dukan ya ga ta juyo ta saitinsa sannan ta fara yunƙurin tashi zaune. Sauke hannun ya yi tana gama daidaituwa a zaune sai ya lura kamar ba cikin da ya bar ta da shi.

Nan da nan wani annuri ya bayyana a fuskarsa har bakinsa na rawa wurin jefa mata tambayar “Ina cikin kuma?”

Hawaye ne ya fara sirnano mata murya ƙasa-ƙasa ta ce “Na yi ɓarinsa ɗazu, bai zo da rai ba.”

Ai kuwa fuskar nan tasa ta ƙara cika da annuri kamar ya daka tsallen murna ya dai kanne.

“Ina gawar ko…?” Ya tambaye ta da annuri a fuskarsa da mamaki zane a allon fuskarta ta ce “Wace gawa?” 

“Uhmm! Ina nufin abin da kika haifan” Ya faɗa da fara’arsa. 

“Na yi flushing ɗin sa.” Ta amsa masa cikin halin ko in kula.

“What? Kina da hankali kuwa?” Ya faɗa da ɗaga murya. Can kuma sai ya yi tunani a ransa, hakan ma ya yi masa daidai ba sai ya sha wata wahala ba wurin binne tayin, haka kuma asirinsa ba zai tonu ba.

A hankali ya zauna a gefen gadon yana yi mata murmushin yaudara. “Shi kenan ya wuce Sweetheart, yanzu me kike so ki ci?”

Gwalala masa ido ta yi tana mamaki ‘Lallai ma mutumin nan, sai a yanzu ne ya tuna ya fita bai bar mata komai ba? Ba ma wannan ba, me ya kawo sauyin yanayinsa cikin ɗan ƙanƙanin lokaci daga jin cewa tayin bai zo da rai ba?’

“Sweetheart ina jin ki, me za ki ci?” Nan ma shiru sai kawai ya miƙe yana ci gaba da faɗar “Na san me ya kamata ki ci, ina zuwa zan ɗan fita na dawo, ba jimawa zan yi ba ki kula mini da kanki please.”

‘Sabon salo kiran Sallah da usur’ Ta faɗa a ranta, a bayyane kuma ta ja wani dogon tsaki ta sake yin kwanciyarta tana ci gaba da mamakin sauyin halaye irin na mijinta.

 Kamar ba shi ba ne Musan da suka zuba soyayya lokacin samartaka, kamar ba shi ba ne masoyinta mai nuna tsantsar kulawa a kanta irin kulawar da take ba wa kowa mamaki ba, kamar ba shi ne ya so ta yake tarairayar ta kamar ƙwai ba, sai dai ta lura tun lokacin da ta fara samun cikin farko a gidansa komai ya rikiɗe zuwa akasinsa.

Can bayan mintuna ashirin sai ga shi ya shigo ɗakin hannunsa riƙe da flask ɗin ruwan zafi da baƙar leda babba. Har a lokacin ba ta tamka shi ba sai kallon sabuwar duniya take yi, ya yi wa kayan masauki a ƙasa ya haɗa mata shayi mai kauri ya miƙe ya koma kitchen ya ɗauko faranti ya juye wainar ƙwan da take leda a kai sa’an nan ya ɗora mata biredi yanka huɗu ya miƙo mata.

Ita dai sai kallon abin take yana tuna mata da rayuwar amarcinsu kafin komai ya sauya.

Har a wannan lokacin mamaki bai bar ta ta iya furta ko kalma ɗaya ba sai karɓar farantin da ta yi ta daidaita zaman ta a gefen gadon ta fara ci, ba don abincin yana yi mata daɗi ba sai don kada yunwa ta illata raunatacciyar gangar jikinta. Da ba don hakan ba iya wulaƙancin da ya yi mata a yau ya isa ya hana ta karɓar duk wani abu da ya fito daga hannunsa, amma ba komai akwai gaba.

Ƙura masa ido ta yi tana zuƙar shayinta a hankali, tana kiyaye da duk wani motsin shi sai murmushi yake zuba mata wanda rabon da ta ga irin sa a fuskarsa tun watanni biyar baya kafin samun cikin. Wani tunani ne ya zo kanta har ba ta san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba.

‘Idan ka san wata ai ba ka san wata ba, lokaci ya yi da zan nuna maka ni ma na iya makirci.’ Ta faɗa a ranta.

Sannu yake ta jera mata har ta kammala ya kwashe kwanukan ya je ƙofa kenan ya juyo ya ce da ita “Ki yi kwanciyarki ki huta sweetheart yau ni zan yi miki wanke-wanke, shara da ma dukkan ayyukan gidan.”

Gyaɗa masa kai kawai ta yi ya fice don har a lokacin mamaki bai bar ta ta iya furta masa ko harafi ba, haka ta kwanta tana ƙissima abubuwa a ranta har bacci mai nauyi ya yi awon gaba da ita.

Ba ita ta farka ba sai wuraren ƙarfe shida na yamma ta ji sauƙi sosai a tattare da yanayinta, a hankali ta sauko daga kan gadon tana bin ko’ina da kallo ɗakin ya yi fes-fes sai tashin ƙamshi yake. 

 Ta fita falo jiri na ta kwasarta tana laluben gun dafawa ta je har tsakar gida ta ga komai ya dawo hayyacinsa ta girgiza kai kawai ta nufi kitchen da laluben bango nan ma dai komai fes a ɗan gefe kan teburi ta hango kuloli guda biyu a ajiye ta nufe su don tabbatar da abin da zuciyarta ke hasasa mata.

Ai kuwa ta tabbata yau girki ya yi musu, ta sauke duban ta kan lafiyayyen tuwon semo da miyar agusi da take hango nama zuƙu-zuƙu a ciki.

A hankali ta yi wata ‘yar dariya mai kama da ta rainin hankali ta ce “Yaya yau ni ka yi wa girki har da nama? Lallai duniya mai yayi.”

Ba ta sake magana ba ta ciro faranti ta ɗebi abincin ta koma falonta ta rufe shi, sai da ta yo buroshi ta watsa ruwa ta sauya kaya ta sha magungunan rage raɗaɗi sannan ta zauna zaman cin abincin.

“Yaya! Yaya!!” Shi kaɗai take yawan maimaita wa lokaci zuwa lokaci tana girgiza kai. Can bayan sallar magariba ta lallaɓa ta ƙwanƙwasa rufin makwafciyarta tare da neman a turo mata yarinyar gidan za ta aike ta.

Yarinyar na zuwa ta tura ta shagon Ubaid mai chemist wanda suka saba mu’amalar magani da shi don ta kirawo mata shi, ta yi hakan ne saboda sanin amince da ke tsakanin shi da mijinta. Da a ce za ta iya fita da da kanta za ta tafi wurin sa saboda zancen da take so su yi sirri ne, fatan ta dai ya karɓa kira ya zo da wuri kafin dawowar maigidan.

Cikin sa’a ‘yar aiken ba ta rufa mintuna talatin da isar da saƙon ba sai ga sallamar shi a ƙofar gida. Da hanzari ta ɗauko robar da suke ajiye magunguna ta zura hijabin ta tana tafe jiri na kwasarta wai a hakan ma da sauƙi kan ɗazu, ta gefen bango ta dinga raɓawa ta yadda da ta ji za ta faɗi sai ta shi a haka har ta je soro. Daga ciki ta tsaya shi ko yana tsaye daga waje.

“Sannu da zuwa Dr, ya aiki da iyali?”

Ya amsa da “Lafiya lau malama, Zinat ‘yar gidan Abbas ce ta ce kina nemana a gida, Allah ya sa dai lafiya? Don da gida ma na nufa kai tsaye sai dai na ce bari na biyo ta nan ban sani ba ko abin gaggawa ne.”

Ta ɗan yi murmushi da sakakkiyar fuska ta ce “Lafiya amma dai ba na ce lau ba, ba na jin daɗi ne ba zan iya fita ba shi ya sa na ce a yi kiran ka ka yi haƙuri na katse maka uzuri, hakan ba raini ba ne buƙatar gaggawa ce.”

“Ba komai Allah ya ƙara afuwa ina jin ki me ke faruwa?”

Hannunta da ke cikin hijabi ta fitar ta buɗe robar hannunta ta ciro wasu sachet biyu na magani ta miƙa masa tana faɗar “Yauwa don Allah Dr wannan za ka duba mini, jiya ne ina fama da matsanancin ciwon mara na aika a sayo mini magani aka ba ni waɗannan sai dai da na sha na ji abin ya daɗa gaba kamar zan mutu me ya janyo hakan?”

Ɗaga sachet ɗin magungunan ya yi saitin fuskarsa da ke akwai hasken kwan lantarki bai sha wahala ba ya ƙura musu ido, ya ɗauki tsawon sakanni yana nazari kafin ya ɗago fuskarsa da tashin hankali ya ce “Subhanallah! A wane chemist ɗin aka sayo miki waɗannan? Waɗannan ai za su iya kisa.”

Ita ma da mamakin ta kalle shi “To suna da illa ne? ka yi mini bayani don Allah.”

“Waɗannan magunguna ai na zubar da ciki ne, kuma na ga an sha su fiye da ƙima wannan tsaf za su iya aika mai ciki lahira idan ba kwana a gaba. Gaskiya idan ke kika sha ki yi gaggawar ganin likita.”

“Uhmm! Na gode sosai Dr, za ka iya tafiya.” Ta faɗa tana karɓar magungunan daga hannunsa.

Har ya juya zai tafi ta dakatar da shi ta hanyar kiran sunansa “Dr! Ya dakata  ba tare da ya juyo ko ya yi magana ba sai ita ce ta  sake furta. “Don Allah ba na son mijina ya san na kira ka nan ko mun yi wannan zancen, ya zamana sirri tsakanina da kai.”

Ya gyaɗa mata kai kana ya ba ta tabbacin ba wanda zai ji ya juya ya tafi cike da ta’ajibin wannan al’amari.

Bayan ɗagawar Dr ta fi mintina biyu dasƙare a gun tana jinjina lamarin maigidan nata, yanzu ashe har tsanarsa da haihuwa ya kai ya iya yin yunƙurin kisa? Eh mana yunƙurin kashe ta ya yi domin ta tabbatar an sanar da shi hatsarin da ke cikin zubar da ko ƙaramin ciki ballantana wanda aka busa masa rai. Da ba don Allah ya taƙaita mata wahala ba to ko da a ce ba ta barzahu a dai-dai wannan lokacin da tana kwance rai a hannun Allah. Ta daɗe da fuskantar ba ya son haihuwa tun daga yanayin yadda mu’amalarsa da ita ke canzawa a lokacin ciki da sanda take lafiya.

Ƙwafa ta yi ta bar gun zuwa ƙofar ɗakinta ta saka tabarma ta kishingiɗa ta tsunduma kogin tunani.

“Shi kam me ya sa ba ya son haihuwa? Da ya san ba ya son haihuwa ya auro ta? Dole da sake a wannan lamarin wai an ba wa mai kaza kai. Idan har ya tabbata haihuwar ce ba ya so kwata-kwata to dole za ta san abin yi, domin Allah ya gani tana da masifar son ‘ya’ya da ganin ita ma ta tara zuri’a musamman da ya kasance su biyu ne kacal a gun mahaifiyarsu.

Can wuraren ƙarfe tara na dare ta jiyo sallamar mijinta yana doso cikin gidan. Iya sallamar kaɗai ta amsa amma ba wani annuri a fuskarta ballantana tarba.

“Sannu da hutawa sweetheart, ya jikin?” Ya faɗa yana yunƙurin zama kusa da ita. Ta ɗan ja jiki daga kishingiɗen da take ta matsa nesa kaɗan. Yi ya yi kamar bai fahimci komai ba ya zauna yana maimaita tambayarsa cikin kulawa. “Ya jikin sweetheart?” “Da sauƙi.” Ta amsa kamar mai ciwon baki.

Baƙaƙen ledojin da ya shigo da su ya ajiye a gefe ya miƙe ya shiga madafa sai ga shi ya dawo da farantai ƙanana guda huɗu ya ajiye.  Fitilar charging da ke ajiye nesa kaɗan da su ya ɗauka ya nufi wani ɗan loko da yake ajiye Generator yana fadar “Bari na tada in ji na ga alamar sarauniyar tawa zafi ya yi mata yawa, ga shi sun ɗauke wutar.”

Ita dai ba ta iya ce masa komai ba sai taɓe baki da bin sa da ido da take yi, a haka har ya kammala tada injin ya dawo ya kwashi kayan da ya zube a kan tabarmar sannan ya kalle ta fuska a sake ya miƙo mata hannu.

“Zo mu shiga ciki ki sha fanka gimbiyata.” Kallon uku saura kwata ta aika masa ta miƙe ba tare da ta saka hannunta a cikin nasan ba ta yi gaba abin ta.

Ba komai ya saka ta yin hakan ba sai don tunowa da wulaƙancin da ya tsula mata ɗazu da safe kafin ya fita. Kamar a majigi ta hango lokacin da ta durƙusa ta ajiye masa kofin kunun gyaɗar da ya ji madara a gabansa, tana kallo ya shanye shi tas. Kallon ƙosan da ke gabansa ta yi, yadda yake ta maiƙo ya sa yawunta ya tsinke ta kai hannu ta ɗauki guda biyu. Cikin zafin nama ya doke hannun har sai da ƙosan suka watse a ƙasa. Ya ƙanƙance ido cikin masifa.

 “Yau ko ke ce sarauniyar makwaɗaitan duniya wallahi ba za ki ci ba. A yi mace sai masifar kwaɗayin tsiya?”

Ɗago kan da ta yi ta ƙura masa ido ne ya sa ya yi kamar wanda ya karanto abin da ke ranta ya ce “Eh ɗin, an hana ki. Da can wani shegen ne ya ce ki ɗauki cikin har ya saka ki tsinannen kwaɗayi? In dai haka cikin yake to Allah ya tsine masa, ba na maraba ba da shi.”

Hawaye masu zafi suka saukar mata a kumatu ta yunƙura ta tashi. Haka ya cinye komai tas, ya gama shiryawa zai fita ta tambaye shi nata abincin, sai cewa ya yi “Shi ba shi da abin ciyar da ita, don wannan tsinannan cin da ta tsira ba a gidansa ba.” Shi ne ta gabatar da ƙorafinta a kan ciwon mara.

Nan da nan ya fita da rawar jiki ya ce zai je ya sayo magani ashe dama ya samu ta yin cuta.

Ta zo daidai nan a tunaninta ta ja dogon tsaki ta yi masauki kan kujerar falo ‘yar zaman mutum biyu. Shi ko sai a lokacin ya sako ƙafa a falon.

“Subhanallah! Sweetheart wa ya taɓa mini ke kike tsaki ke kaɗai?”

Da ya san irin maƙaƙin baƙincikin da take ji idan ya kira ta da sweetheart ko duk wani suna mai nuna soyayya a yanzu da ya daina wahalar da kansa da son ya burge ta ta wannan hanyar.

“Ba komai.” Shi kaɗai ne amsar da ta ba shi.

Ya zauna yana zazzage kazar da ya zo da ita a kan farantai biyu. Da kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta ce da shi “Ni kam yaya ɗazu wane kalar magani ne ka sayo mini?” 

A diririce ya ɗago kansa ya zuba mata idanunsa ma su nuna tsantsar rashin gaskiya “Ma…ma…maganin ciwon da kika tambaya mana, me kika gani?” 

Ta kafe shi da ido, a iya saninta da shi ba ya in-ina, amma da ke an ce mara gaskiya ko cikin ruwa ya yi jiɓi, sai ga shi ya fara a yau.

Ɗan guntun murmushi ta yi kana ta ce “Ai yaya da na sha maganin nan ƙiris ya rage ban mutu ba, ni fa ina ganin kamar da gangan masu Kyamis ɗin suka ba ka shi don su kashe maka mata. Na fi zargin ma shi ne ya tado naƙudar kuma ya janyo mutuwar ɗan.”

Saurin sunkuyar da kansa ƙasa ya yi jikinsa ya yi sanyi har ya kasa ƙarasa juye kankanar da ya fara, tsawon sakanni suka shuɗe da su a hakan kafin ya ɗago ya buɗe baki da nufin yin magana.

“Uhm! Aiko in dai haka ne zan koma na ji dalilinsu na wannan yunƙurin, wallahi ba zan yarda ba, a kashe mini abar ƙauna? Ina! Dole sai na ji dalili.” 

A fusace ya miƙe da nufin zai fita wai zai je yin rigima da masu magani.

Dariyar yaƙe ta yi kafin ta ce “Manta da su, ai ya riga ya wuce, idan ma za ka musu maganar ka bari sai gobe, shi ma amfanin ta su san an sani domin su kiyaye gaba kada su ɗauka ba a ankara ba su sake jarrabawa domin ba za ta yi musu kyau ba a gaba.”

Bai ce komai ba sai dai ya ji a ransa kamar saƙon shi ake turawa a fakaice.

“Am! Don Allah yaya ara mini wayarka na kira mamanmu.”   

Ya yi saurin ɗagowa ya watsa mata idanunsa.

“Me ye dalilin kiran?”

“Haba yaya! Mahaifiyata ce fa, shi ne har sai an nemi dalilin kiran? To gaisawa za mu yi.”

Ya saka hannunsa ya ɗauki yanka ɗaya na kankana ya kai baki kafin ya ce “Na ji zan ba ki, amma da sharaɗi.” Kasa magana ta yi kawai ta saki laɓɓa tana kallonsa.

Jin shiru ya sanya ya ci gaba. “A gabana za ki yi duk hirar da za ki yi don kar ki cinyen kati.”

Daidai lokacin ya saka hannu a aljihun gaba ya ciro wayar ya cire pin ya miƙa mata. Miƙewa ta yi da wayar a hannu tana mayar da numfashi, ta fara neman layin.

“Ina za ki je kuma? Ba ki ji sharaɗina ba ne.” 

Murmushin da ita kaɗai ta san ma’anarsa ta wurga masa kana ta fara takawa zuwa uwar ɗaka tana faɗar “Ai ina da credit a layina da ke cikin wayar zan kira ta da shi, shi kenan?”

Ba tare da ta jira amsar shi ba ta ci gaba da tafiya, yana jin lokacin da aka ɗaga wayar ta ce “Assalamu alaikum inna!” 

Jiyojin jikinsa gabaɗaya suka sage ba don yana son hana ta zumunci da iyaye ko danginta ba ne, a’a ya dai hana ta riƙe waya ne don kada ta dinga ɗibar sirrinsa da na gidansa tana fesa wa danginta da suke wata uwa duniya. Saboda ya sani suna matuƙar ganin girma da darajar shi, ba ya son ta zubar masa da wannan ƙimar a idonsu.

Zaunawa ya yi yana ta saƙe-saƙe a ransa…

Ummu Intisar ce

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here