Home Siyasa Atiku ya yaba da hukuncin kotu kan shugabancin ADC

Atiku ya yaba da hukuncin kotu kan shugabancin ADC

2
0

Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yabawa babbar kotun tarayya da ke Abuja bayan ta yi watsi da ƙarar da aka shigar tana ƙalubalantar shugabancin jam’iyyar, yana mai cewa hukuncin nasara ce ga dimokuraɗiyya da bin doka.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan hulɗa da jama’a, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce hukuncin da Mai Shari’a Musa Liman ya yanke ya tabbatar da cewa rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyun siyasa ya kamata a warware su bisa kundin tsarin mulkinsu da hanyoyin sulhun cikin gida.

Ya zargi wasu masu ruwa da tsaki da ƙoƙarin raunana jam’iyyun adawa ta hanyar amfani da ƙorafe-ƙorafe a kotu da kuma wasu cibiyoyi, amma ya ce hukuncin ya nuna cewa ɓangaren shari’a ba zai amince a mayar da shi kayan aikin siyasa ba.

Atiku ya kuma jaddada cewa kwamitin gudanarwar ADC ƙarƙashin jagorancin David Mark ya samu shugabanci ne bisa doka da kundin tsarin mulkin jam’iyyar. Ya buƙaci mambobin ADC su ci gaba da haɗin kai tare da mayar da hankali kan shirye-shiryen zaɓen shekarar 2027, yana mai cewa jam’iyyar na da ƙwarin gwiwar zama madadin gwamnati ga ‘yan Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here