Mataimakin ɗan takarar jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya bayyana cewa tsofaffin gwamnonin Kano, Ibrahim Shekarau da Abdullahi Ganduje, da kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf, sun rasa karfin siyasa a jihar.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Abuja, inda ya ce siyasar da aka gina bisa “cin amana” ba ta daɗewa.
Ya ce rikicinsa da Ganduje ya fara ne lokacin da tsohon gwamnan ya fara ƙalubalantar tsarin siyasar da suka gina tare, yana mai cewa hakan ya janyo koma bayan siyasarsa.
Game da Gwamna Abba Yusuf, Kwankwaso ya ce shi da magoya bayansa sun yi aiki tukuru wajen tabbatar da nasarar Abba Kabir Yusuf a zaɓen 2023, amma daga baya gwamnan ya nisanta kansa daga ƙungiyar siyasar da ta taimaka wajen ɗora shi kan mulki.
Kwankwaso ya kuma zargi Abba Yusuf da ƙoƙarin maye gurbinsa a matsayin jagoran siyasar Kano, yana mai cewa lokaci ne zai tabbatar da sakamakon irin waɗannan matakai.
Ya ƙara da cewa sauyin alaƙar ’yan siyasa da tsoffin abokan hulɗarsu ba sabon abu ba ne a Najeriya, sai dai ya ce abin da ya faru a Kano ya fi fice.






