Home Siyasa Rangwamen Man Fetur Na Kwana 30 Ba Zai Magance Wahalar ’Yan Najeriya...

Rangwamen Man Fetur Na Kwana 30 Ba Zai Magance Wahalar ’Yan Najeriya Ba – Inji Atiku

18
0

Rangwamen Man Fetur Na Kwana 30 Ba Zai Magance Wahalar ’Yan Najeriya Ba – Inji Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya soki shirin Gwamnatin Tarayya na rage farashin man fetur na tsawon kwanaki 30 a gidajen mai na NNPC.

Atiku ya bayyana matakin a matsayin rangwame na wucin gadi, yana mai cewa ba zai magance matsalar tsadar man fetur da ta jefa ’yan Najeriya cikin mawuyacin hali ba.

A cikin wata sanarwa da Phrank Shaibu, Daraktan Sadarwa na Dabarun Yaƙin Neman Zaɓen ADC, ya fitar, Atiku ya ce bai dace a yi amfani da rangwamen man fetur na wata ɗaya a matsayin hanyar jan hankalin jama’a ba.

Ya ce ’yan Najeriya sun shafe tsawon lokaci suna fuskantar matsin tattalin arziki, don haka rangwamen na ɗan lokaci ba zai sa su manta da wahalhalun da suka sha ba.

“’Yan Najeriya ba wawaye ba ne da za a ba su rangwamen man fetur na wata ɗaya bayan shekaru suna fama da tsadar mai, sannan a sa ran za su manta da wahalhalun da suka sha bayan rangwamen ya ƙare,” in ji Atiku.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here