Home Labarai Nijeriya: Siyasa daban, addini daban— Sanusi

Nijeriya: Siyasa daban, addini daban— Sanusi

23
0

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da a fayyace bambanci tsakanin harkokin addini da siyasa a Najeriya.

Sanusi ya bayyana haka ne a Abuja yayin gabatar da littafin Military Transformational Leadership in Action: The Buratai Era.

Ya ce ’yan siyasa su mayar da hankali kan mulki, ilimi, lafiya da bunkasar tattalin arziki, yayin da malaman addini su kula da ayyukan addini.

Sarkin ya ce cudanya tsakanin addini da siyasa na kara rura wutar rarrabuwar kawuna tsakanin ’yan Najeriya bisa kabila, yanki da addini, lamarin da zai iya haifar da karin rikice-rikice.

Ya kuma bukaci a daina mayar da manyan hukumomin kasa kamar sojoji, ’yan sanda, Babban Bankin Najeriya (CBN), bangaren shari’a da kafafen yada labarai kayan siyasa.

A cewarsa, wadannan hukumomi suna bukatar samun ‘yanci domin su iya sa ido kan harkokin siyasa da kare muradun kasa na dogon lokaci, maimakon mayar da hankali kan zagayen mulki na shekaru hudu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here