Home Siyasa Dalilin da ya sa Aisha Buhari ta ziyarci Atiku a Abuja

Dalilin da ya sa Aisha Buhari ta ziyarci Atiku a Abuja

12
0

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya karɓi bakuncin uwargidan marigayi Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari, a gidansa da ke Abuja.

Atiku, wanda ke takarar shugabancin Najeriya a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, ya bayyana ziyarar Aisha a matsayin mai cike da muhimmanci.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku bai bayyana dalilin ziyarar ba, sai dai ya ce ta tunatar da masu neman kyakkyawar Najeriya muhimmancin fifita jin daɗin al’umma, mutuncinsu da makomarsu.

Ya ce iyalai da dama a faɗin ƙasar na fama da tsadar abinci, sufuri, ilimi, kiwon lafiya da sauran abubuwan buƙata na yau da kullum.

Atiku ya ce Najeriya na buƙatar tattalin arzikin da zai ba wa mutane damar cin moriyar ƙoƙarinsu, da kuma samar da damammaki domin iyalai su rayu cikin mutunci da fata.

Ya ce: “Dole ne mu rage wa al’umma nauyi, mu dawo da bege, sannan mu gina Najeriya mai sauƙin rayuwa ga kowa.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here