Gwamnatin Sakkwato ƙarƙashin jagorancin Dakta Ahmad Aliyu ta kafa kwamitin malamai 14 domin duba lamarin hatsaniya da ta faru a jihar wanda kalamai masu nasaba da addini suka haifar.
Gwamnatin Sakkwato ta ba da sanarwar kafa kwamitin a wata takarda da daraktan yaɗa labarai a fadar gwamnati Abubakar Bawa ya sanyawa hannu ya ce Sarkin Malaman Sakkwato Malam Yahaya Na Malam Ɓoyi ne shugaban kwamitin in da Barista Gandi Umar Muhammad ne Sakatare.
Sauran Mambobin kwamitin sun haɗa da Malam Muhammad Isa Talatar Mafara da Farfesa Mansur Ibrahim da Farfesa Mansur Ibrahim Sa’id da Malam Lawal Maidoki da Malam Bello Na Malam Ɓoyi da waƙili daga Izala Jos da Izala Kaduna da waƙili a Jama’atu Nasril Islam da waƙili a majalisar Sarkin Musulmi da waƙili a Tijjaniya da Ƙadiriyya da Kwamishinan ma’aikatar harkokin addinin musulunci.
“An baiwa Kwamitin kwana 14 ya gabatar da rahotonsa.”
Ya ce Gwamnati ta buƙaci kwamitin ya gabatar da bayani mai zurfi kan matsayar Shari’a a bayanan da Malam Musa Lukuwa ya bijiro da su, a kuma baiwa gwamnati shawara kan abin da yakamata ta yi.
