Daga Yahaya Mahi Na Malam Babba
Masarautar Kaura Namoda ta bayar da tallafin kayan abinci ga mutane 1,000, kuɗin cefane, tare da tallafin karatu ga wasu mutane 30, waɗanda dukkansu ‘yan asalin masarautar ne.
An gudanar da wannan shiri ne a yayin bukukuwan murnar karɓar sandar sarauta da bikin Askin Sarauta na Mai Martaba Sarkin Kiyawan Kaura Namoda, Major Dr. Sanusi Muhammad Ahmad Asha (Khadimul Qur’an), wanda Mai Girma Gwamnan Jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal, ya miƙa masa sandar sarautar.
Da yake jawabi kan wannan tallafi, Mai Martaba Sarkin Kiyawan Kaura Namoda ya bayyana cewa an samar da tallafin ne domin taimaka wa al’umma wajen sauƙaƙa musu rayuwa, musamman masu ƙaramin ƙarfi da sauran mabukata a cikin masarautar.
Ya kuma bayyana cewa tallafin karatun da aka bayar ga mutane 30 na daga cikin ƙoƙarin tallafa wa harkokin ilimi da bunƙasa rayuwar al’ummar masarautar.
A nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Nasarawa, Dr. Ibrahim Usman Jibril, CON, wanda ya sanya wa taron albarka, ya bayyana farin cikinsa da samun damar halartar wannan biki.
Ya bayyana cewa duk da kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninsa da Masarautar Kaura Namoda, wannan ne karon farko da ya samu damar ziyartar masarautar domin taya ta murnar wannan gagarumin ci gaba.
Haka kuma, ya yi addu’ar samun zaman lafiya mai ɗorewa a Kaura Namoda da Jihar Zamfara baki ɗaya, tare da roƙon Allah Ya kawo ƙarshen matsalolin tsaro da ke addabar yankin.
Taron ya samu halartar manyan baki da dama, ciki har da wakilin Sarkin Bauchi, Sarkin Awe, Dr. Isah Abubakar Umar, Sarkin Kanje, Shugaban Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda, Hon. Mannir Mu’azu Haidara, da wasu daga cikin ‘yan Majalisar Masarautar.
Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Hakimai, Dagatai, uwayen ƙasa, shugabannin ƙungiyoyi da sauran al’umma masu kishin masarautar.
