Home Siyasa Lagos da Kano da Kaduna ne kan gaba wajen yawan masu katin...

Lagos da Kano da Kaduna ne kan gaba wajen yawan masu katin zaɓe – INEC

12
0

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewa Lagos, Kano da Kaduna ne jihohin da suka fi yawan masu rajistar kada kuri’a a Najeriya gabanin babban zaben 2027.

Shugaban INEC, Joash Amupitan, ya ce adadin masu rajistar kada kuri’a a fadin kasar ya kai miliyan 110.

Ya bayyana cewa Lagos ce ke kan gaba da masu kada kuri’a 7,488,633, sai Kano da 6,570,276, sannan Kaduna da 4,662,640.

Katsina ce ta zo ta hudu da 3,876,051, sai Rivers da 3,736,434, Oyo da 3,588,111, Delta da 3,525,988, Benue da 3,057,225, Ogun da 3,037,981, yayin da Bauchi ta cika jerin jihohi 10 na farko da 3,012,547.

Amupitan ya ce alkaluman sun kunshi bayanan rajistar masu kada kuri’a daga matakai uku da hukumar ta gudanar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here