Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Sakkwato ta kammala sauraren ƙarar da Sanata Sahabi Ya’u Ƙaura ya shigar domin ƙalubalantar hukuncin babbar Kotun Tarayya dake Gusau wadda ta soke sahihancin zaɓen fidda gwani da ya ba shi nasara a farko.
Bayan jin bahasi daga kowane ɓangaren mai ƙara da wanda ake ƙara Alƙalan su uku sun sanar da za su faɗi ranar da za su yanke hukuncin kan maganar zaɓen fitar da gwanin na Sanatan Zamfara ta Arewa.
Lauyan wanda ake ƙara Barista Bello Galadi ya bayana abin da ya faru a kotu ya ce “ni ne waƙilin wanda ake ƙara na farko waton Sani Abdullahi Shinkafi, a yau(Talata) kowa ya ba da bayaninsa na ƙarshe a gaban kotun ɗaukaka ƙara da aka shigar, domin shi wanda ya kawo maganar bai gamsu da hukuncin farko ba, a yanzu kowa ya ba da bahasinsa kotu ta ce za ta sanar da ranar yanke hukunci domin a ji matsayarta.”
Galadi ya ƙara bayanin kan abin da ya haifar da shari’ar ya ce “zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar APC a Zamfara ta Arewa ne muka ce ba a gidanar da shi ba suka ce an yi a haka ne muka garzaya kotun tarayya ta Gusau kuma ita ta gamsu da abin da muka gaya mata, zaɓen ya ci karo da dokokin ƙasa dana hukumar zaɓe dana jam’iya, su kuma da ba su gamsu ba suka ɗaukaka ƙara, lamarin ya tsaya ne zaɓen na fitar da gwani da aka yi a 19/05/2026.
“Muna fatan wannan kotun ta yi mana adalci kamar yadda ta ƙasa ta yi mana domin gaskiyar mu a bayyane take kuma mun san za a kai ga gaskiya, a ranar da za a yanke hukuncin,” a cewar Barista Galadi.
Dakta Sani Abdullahi Shinkafi bayan fitowa kutun ya ce sun zo ne kan ƙarar da Sanata Ƙaura ya shigar da su, shi da jami’iyar APC da hukumar zaɓe domin ba da bahasi, yana da tabbacin sake nasara a kotun ɗaukaka ƙara, “gaskiya sunanta gaskiya haka ma ƙarya sunanta ƙarya kowa yasan ba a yi zaɓe ingantacce a Zamfara ta Arewa ba, wasu ‘yan tsiraru ne suka rufe kansu a ɗaki suka yi ɗoki ɗora in da suka samu matsala magoya bayan APC da suka yi rijista ba su wuce 26,000 amma suka ayyana wanda ya yi nasara da ƙuri’u 65,000 ina hankali ke ɗaukar wannan mun ba da ingantattun sheda gaban kotu bisa ga tsarin doka.”
“Matsayina na shugaban talakawa da ke waƙiltarsu muna faɗa da ɗoki ɗora da walaƙanta mutane, mun yi ɗamara a 2027 sai mun sauya waɗanda suka mayar da kujerar Sanatan Zamfara ta Arewa kayan gado. A Zamfara ba wani da ke ɗaukar nauyin shari’ata nafi ƙarfin wani ya yi amfani da ni, kowa yasan aƙidata,” a cewar Dakta Shinkafi






