Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta soke hukuncin babbar kotun tarayya da ya umarci hukumar zaɓe ta kasa (INEC) ta cire rajistar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) da wasu jam’iyyu huɗu kamar yadda jaridar Vanguard ta rawaito.
Kotun, a hukuncin da alkalai uku suka yanke baki ɗaya, ta ce babbar kotun tarayya ba ta da hurumin sauraron shari’ar, saboda ƙarar da aka shigar ba ta cika ka’idojin doka ba. Ta kuma bayyana cewa babu ingantacciyar ƙara da za ta ba da damar umarnin cire rajistar jam’iyyun.
Kotun ta ce alkalin babbar kotun ya yi watsi da hujjojin da suka nuna cewa jam’iyyun sun taɓa lashe kujeru a zaɓukan baya, tare da yin hukunci duk da umarnin dakatar da ci gaba da sauraron shari’ar da kotun ɗaukaka ƙara ta bayar.
Saboda haka, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da cewa jam’iyyun da abin ya shafa har yanzu suna da cikakkiyar rajista. Jam’iyyun sun haɗa da ADC, Action Peoples Party (APP), Action Alliance (AA), Accord Party (AP) da Zenith Labour Party (ZLP).
Tun da farko, Babbar Kotun Tarayya ta umarci INEC ta cire rajistar jam’iyyun biyar, tare da hana su shiga harkokin zaɓen 2027, bayan ƙungiyar National Forum of Former Legislators (NFFL) ta yi zargin cewa sun gaza cika sharuddan kundin tsarin mulki na ci gaba da kasancewa a matsayin jam’iyyun siyasa. Sai dai dukkan jam’iyyun da INEC sun ɗaukaka ƙara, lamarin da ya kai ga soke hukuncin.






