Babbar Kotun Jihar Kaduna ta yi watsi da bukatar beli da tsohon gwamnan jihar, Nasir Ahmed El-Rufai, ya gabatar a shari’ar da ake yi masa kan zargin cin zarafin ofis da wasu laifuka masu alaƙa da rashawa.
Alkalin kotun ya yanke hukuncin ne yayin da ake ci gaba da sauraron shari’ar da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta kasa (ICPC) ta shigar, inda ake zargin El-Rufai da hannu a wasu laifuka da suka shafi tafiyar da harkokin gwamnati a lokacin mulkinsa na gwamnan Jihar Kaduna.
Sai dai tsohon gwamnan ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa, yana mai jaddada cewa zai kare kansa a gaban kotu. Ana sa ran ci gaba da sauraron shari’ar a kwanaki masu zuwa.






