Jam’iyyar NDC ta ce ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotun da ya soke rajistarta, tare da neman a dakatar da aiwatar da hukuncin har sai an kammala sauraron ƙarar.
Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da jagoran jam’iyyar, Sanata Henry Seriake Dickson, ya wallafa a ranar Litinin 29 ga Yuni, 2026.
Ya ce jam’iyyar ta miƙa takardun ɗaukaka ƙarar da kuma buƙatar dakatar da aiwatar da hukuncin ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).
Ya ƙara da cewa jam’iyyar na ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen zaɓe, inda aka fara loda sunayen wasu daga cikin ‘yan takararta a shafin INEC.
Ya kuma bayyana cewa jam’iyyar za ta ci gaba da bin duk tanade-tanaden jadawalin zaɓen da INEC ta fitar, tare da bayyana cewa babu dalilin da zai sa magoya bayan jam’iyyar su firgita.
Haka kuma ya yi kira ga ɓangarorin da abin ya shafa su mutunta tsarin dimokuraɗiyya da doka.






