Home Kiyon Lafiya Gwamnatin Sakkwato za ta saye motocin daukar marasa lafiya 244

Gwamnatin Sakkwato za ta saye motocin daukar marasa lafiya 244

12
0

Gwamnatin Sakkwato za ta saye motocin daukar marasa lafiya 244

Gwamanatin Sakkwato za ta saye motocin ɗaukar marar lafiya ga ƙananan asibitoci guda 244 dake faɗin jihar domin samun bunƙasar kiyon lafiya.Gwamnan Sakkwato Alhaji Ahmad Aliyu ya sanar da hakan a lokacin sauraren ra’ayin jama’a kan kasafin kuɗi na shekarar 2027 da za a gabatar a gaban majilisar dokokin jiha, ya ce a cikin manyan asibitoci 23 sun gyara 21 tare da gyaran kananan asibitoci 192 cikin 244.Gwamnan ya ba da sanarwar shirin sauya wurin zaman babbar asibitin ƙwararru ta jiha in da za ta koma asibitin Murtala sai asibitin mata da ƙananan yara ta Maryam Abacha ta dawo in da asibitin ƙwararrun ta tashi.Ahmad Aliyu a lokacin da yake karɓa tambayoyi ga mahalarta taron ya bayyana cewa sauya wuraren za a yi shi ne domin ƙara inganta harkokin lafiya da kawar da ƙalubalen muhali da ake fama da shi a wuraren.Ya nuna damuwarsa kan wurin da asibitin Marym Abacha waton kusa ga tsohuwar Kasuwa da tashar mota gwamnan ya nemi masana da su yi nazari su ba da mafita kan ƙudirin.Hukumar kula da kananan yara ta UNICEF ta bayyana nasarar da kasafin na 2026 ya samu ba ta wuce 33.3 zuwa karshen watan Satumba, ta roƙi gwamnati ta riƙa kula da lokaci a kasafin kuɗin da ya shafi harkar ci-maka ta yara da lamurran jama’a da suka shafi kananan hukumomi da faɗaɗa harkar inshoran lafiya.A jawabin maraba Kwamishina a ma’aikatar kasafi da bunkasa tattalin arzikin jiha Dakta Bashir Achida ya ce gwamnatin Ahmda Aliyu ta himmatu wajen aiwatar da tsare-tsaren bunƙasa tattalin arziki da zai kawo cigaba a jihar Sakkwato.”Tun sanda gwamnan Sakkwato ya soma aiki yake gudanar da wannan aikin na jin bahasain mutane kan abubuwan da suke bukata a sanya a kasafin kudi domin aiwatarwa da za su kawo cigaban jiha a dukkan mazabu da yankuna.”  

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here