Bayanai sun nuna cewa wasu manyan ’yan siyasa a jam’iyyun adawa a Nijeriya, ciki har da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar; takwaransa na jam’iyyar NDC Peter Obi, har ma da Seyi Makinde na APM, za su gana a Abuja ranar Litinin domin ci gaba da tattaunawa kan haɗa kan ’yan adawa domin fuskantar Shugaba Bola Tinubu.
Ana kuma sa ran ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PRP, Donald Duke, zai halarci taron, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Taron, zai mayar da hankali kan sake ƙoƙarin daidaita bambance-bambancen ra’ayoyi da samar da dabarar bai ɗaya gabanin babban zaɓen 2027.
A gefe guda kuma, jam’iyyar APC ta bayyana kwarin gwiwar cewa ƙawancen da ’yan adawa ke ƙoƙarin kafawa ba zai shafi damar Shugaba Tinubu na samun wa’adi na biyu ba.
