Home Siyasa Duk masu shirin magudi a zaɓen 2027 za su sha mamaki- Lawan...

Duk masu shirin magudi a zaɓen 2027 za su sha mamaki- Lawan Daura

15
0

Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Allied Peoples’ Movement (APM), Lawal Daura, ya ce ba za a bari a ci zaɓen 2027 ta hanyar magudi ba.
Daily Trust ta rawaito cewa Daura ya bayyana hakan ne a ranar Talata, yayin ƙaddamar da Kwamitin Gudanar da Yaƙin Neman Zaɓen Ƙasa (NCMC) na Ƙungiyar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta Makinde-Daura (MDPCO).
A cewar tsohon Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta Fararin Kaya (DSS), za a yi duk mai yiwuwa a dakile duk wani yunƙuri na yin magudi a zaɓen 2027.
Ya ce waɗanda ke shirin yin magudin zaɓen 2027 za su sha mamaki. Abin mamaki na nan tafe gare su.”
Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasar ya kuma ce adadin masu rajistar zaɓe a Najeriya ya haura miliyan 100, yana mai bayyana wannan adadi a matsayin muhimmi ga zaɓen 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here