Shugaban jam’iyyar ADC na kasa, David Mark, ya ce jam’iyyar za ta bi dokokin zabe a babban zaben 2027, amma ba za ta amince da duk wani yunkurin magudin zabe ba.
Mark ya bayyana haka a Abuja lokacin da shugabannin Savannah Centre for Diplomacy, Democracy and Development, karkashin jagorancin tsohon Alkalin Alkalai na Najeriya, Olukayode Ariwoola, suka ziyarci hedikwatar ADC.
Ya ce ADC ta kuduri aniyar gudanar da siyasa cikin gaskiya da mutunta dimokuradiyya, amma za ta yi tsayin daka wajen kare hakkinta idan aka yi yunkurin yin magudi.
A nasa bangaren, Ariwoola ya bukaci shugabannin ADC da su tabbatar da cewa ‘yan takararta da magoya bayanta sun bi dokokin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), tare da kauce wa duk wani abu da ka iya haddasa rikicin siyasa.





