Duk da kuɗaɗen da gwamnatin Ahmad Aliyu ta samu cikin shekara 3, jama’a ba su ga canji mai kyau ba – Ɗan takarar gwamna na ADC a Sokoto
Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar ADC a jihar Sakkwato, Manir Muhammad Dan’Iya, ya ce duk da dimbin kuɗaɗen da gwamnatin jihar da ƙananan hukumomi suka samu cikin shekaru uku da suka gabata, har yanzu al’ummar jihar ba su ga ci gaban da ya dace ba.
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaransa, Aminu Abdullahi ya fitar, Dan’Iya ya ce ya kamata a auna nasarar gwamnati da tasirin da take yi ga rayuwar jama’a, ba da jawabai ko tallata manufofi kawai ba.
Ɗan takarar gwamnan ya yi zargin cewa matsalolin tsaro da ƙarancin ruwa da tabarbarewar ilimi da lafiya na ci gaba da addabar al’ummar jihar duk da albarkatun da gwamnati ke samu.
Ya kuma yi suka ga tsare-tsaren gwamnatin jihar guda 9, yana mai cewa mazauna jihar da dama har yanzu ba su ga sakamakon da ya dace daga manufofin ba.
Duk da kuɗaɗen da gwamnatin Ahmad Aliyu ta samu cikin shekara 3, jama’a ba su ga canji mai kyau ba – Ɗan takarar gwamna na ADC a Sokoto
