Home Siyasa Dalilin da ya sa INEC ta tsawaita wa’adin rijistar masu zaɓe

Dalilin da ya sa INEC ta tsawaita wa’adin rijistar masu zaɓe

15
0

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce ta tsawaita wa’adin aikin ci gaba da yin rajistar masu zaɓe da ake gudanarwa a faɗin ƙasar nan da ƙarin mako biyu, domin bai wa ƴan Najeriya da suka cancanci yin rajista amma ba su samu damar yin hakan ba ƙarin lokaci, musamman matasan da suka cika shekara 18.

Mai magana da yawun INEC, Zainab Aminu Abubakar, ta shaida wa BBC cewa an fara aikin rijistar ne a matakai daban-daban tun a watan Agustan shekarar 2025, kamar yadda Jaridar Daily trust ta ruwaito.

Ta bayyana cewa, tun da farko an tsara kammala aikin rijistar a ranar 10 ga Yuli, 2026, amma bayan ƙorafe-ƙorafe da kuma son a ƙara lokaci daga jam’iyyun siyasa, ƙungiyoyin farar hula da sauran al’umma, hukumar ta yanke shawarar tsawaita wa’adin, inda tace yanzu aikin rijistar zai ƙare ne a ranar 26 ga Yuli, 2026.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here