Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya ce ziyararsa zuwa United States za ta maida hankali kan tabarbarewar tsaro, tattalin arziki da shugabanci a Najeriya.
Ya bayyana cewa ƙasar na cikin babban rikici, inda kashe-kashe da garkuwa da mutane ke ƙaruwa, yayin da tattalin arziki ke ƙara muni sakamakon hauhawar farashi da faɗuwar darajar kuɗi.
Atiku ya kuma gargadi gwamnati ta gyara alkiblarta, tare da kira ga ‘yan Najeriya su tashi tsaye su nemi a yi musu adalci.






