Home Labarai BUA ya ba da tallafin kayan noma na miliyan 100 a Sakkwato

BUA ya ba da tallafin kayan noma na miliyan 100 a Sakkwato

8
0


Kamfanin Siminti na BUA  ya raba kayan noman damina da kudinsu ya kai miliyan 100 ga manoma 211 da ke kauyukkan da ke zagaye da kamfanin a cikin shirinsa na taimakawa rayuwar mutane.Shirin an samar da shi ne domin bunkasa samar da abinci da taimakon manoman da aka sauyawa gonaki da matsugunni don tabbatar da ba su ta gaiyara ba.A lokacin da yake magana wurin rabon tallafin a ranar Assabar Babban Darakta na kamfanin Injiniya Yusuf Binji ya tabbatar da kudirinsa na cigaba da tallafawa talakawan kauyukkan dake zagaye da kamfanin musamman wadanda aka sauyawa wurin zama.Mataimakin Darakta a hulda da jama’a Alhaji Sada Suliman ya wakilce shi  ya ce shirin an samar da shi ne domin rage radadin sauya wurin zama da bunkasa noma don samar da walwala a tsakanin wadanda suka ci gajiyar lamarin.”Kulawarmu na kan mutanen da aiyukkanmu suka shafa don tabbatar da an taimakawa rayuwarsu ta zama mai amfani, su yi noma, su kara inganta inda suke zaune.” Da farko Daraktan lafiya na kamfanin Ali Gumel ya yi kira ga wadanda suka ci gajiyar su yi amfani da abin da aka ba su yanda yakamata.Gumel ya sanar cewa Kamfanin BUA ya himmatu wurin bunkasa harkar noma, kan haka ya yi hadaka da hukumar bunkasa hakar noma ta jiha(SADP) in da za a horar da dukkan mutanen da ta baiwa tallafin sanin  dubarun noma don samar amfanin gona mai yawa da inganci.

A lokacin da yake tabbatar  da hadakar Manajan SADP Alhaji Abubakar Danmaliki ya baiwa manoman tabbaci za a cigaba da sanar da su abubuwan da zasu taimake su, da ziyatar su akai-akai don tabbatar da sun ci gajiyar ilmin da suka koya.

Da yake fadin kayan da suka samu Alhaji Rabi’u Maska ya ce an raba buhun taki NPK 422 da UREA 211 da Kwantena 211 na daskararren takin zamani da maganin kashe haki da kwari da yawansu ya kai 50kg, da irin shinkafa da masara da gero da dawa da gyada da Zogala.

Wadanda suka ci gajiyar kayan sun yi godiya ga kamfanin, sun ce kayan son zo  a kan lokaci da yanayin da ake bukatarsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here