Sojojin yanki na Takwas da ke cikin Rundunar Fansan Yamma sun yi nasarar dakile wani harin kwantan bauna da ‘yan bindiga suka kawo a Sakkwato.
A cewar bayanin sirri na Sojojin batagarin a Kwanar Jalof, a kauyen Jangeru dake cikin karamar hukumar Shinkafi ta Zamfara suka yi yunkurin kaiwa mutane hari.
Sun yi nasarar kwato makamin PKT da babur guda biyu, kakin soja guda 8.






