Rundunar ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja ta bayyana cewa bidiyon Peter Obi da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta tsohon bidiyo ne, kuma an gurɓata shi da saƙonnin siyasa domin ya ba da ma’anar da ba ta dace ba.
Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar a ranar Litinin 29 ga Yuni, 2026.
Rundunar ta ce bidiyon ya samo asali ne daga wani lamari da ya faru a shekarar 2024 lokacin da jami’an rundunar suka kai ɗauki hedikwatar Jam’iyyar Labour da ke Utako bayan samun rahoton rikici a jam’iyyar.
Sanarwar ta ƙara da cewa Peter Obi ya yi magana da jami’an ‘yan sandan ne yayin da suke gudanar da aikinsu, ba domin wani gangamin siyasa ko neman goyon bayansu ba.
Kazalika, sanarwar ta bayyana cewa Kwamishinan ‘Yan Sandan Abuja ya ba da umarnin gudanar da bincike kan yadda aka gurɓata bidiyon.






