Home Siyasa 2027: ADC ta zargi Kwankwaso da yi wa Tinubu aiki

2027: ADC ta zargi Kwankwaso da yi wa Tinubu aiki

8
0

Kwamitin yakin neman zaben shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC ya bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, zai iya lashe jihar Kano a zaben shugaban kasa na 2027 ba tare da goyon bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ba.

Kwamitin ya zargi tsohon gwamnan Kano da kokarin haddasa rabuwar kai tsakanin ‘yan adawa domin taimaka wa Shugaba Bola Tinubu samun wa’adi na biyu.

A cikin wata sanarwa da daraktan yada Labarai da Hulda da Jama’a na kwamitin, Kola Ologbondiyan, ya fitar, ADC ta soki kiran Kwankwaso na cewa Atiku ya janye wa Peter Obi takarar shugaban kasa.

Ologbondiyan ya ce maimakon Kwankwaso ya kalubalanci gwamnatin Tinubu kan matsalolin tsadar rayuwa, yunwa, talauci da rashin tsaro, sai ya mayar da hankali kan sukar Atiku.

Ya kuma yi nuni da nasarorin da tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ya samu a Kano a zaben 2003 da 2007, yana mai cewa nasarar Atiku ba ta dogara da goyon bayan Kwankwaso kadai ba.

Jigo na ADC din ya kara da cewa Atiku yana da karfin siyasa a fadin Najeriya, sabanin Kwankwaso wanda ya ce mafi yawan karfinsa yana cikin Kano.

Ya kuma tunatar da cewa Kwankwaso ya zo na hudu a zaben shugaban kasa na 2023, yana tambayar ko zai iya mayar da tasirinsa na Kano zuwa nasara a matakin kasa.

Sai dai kwamitin ya bukaci ‘yan adawa su ajiye bukatunsu na kashin kai, su hada kai domin kayar da jam’iyyar APC a zaben 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here