Home Siyasa ADC ta ƙalubalanci naɗin ɗan’uwan Gwamnan Sokoto a matsayin Kwamishinan INEC da...

ADC ta ƙalubalanci naɗin ɗan’uwan Gwamnan Sokoto a matsayin Kwamishinan INEC da Tinubu ya yi

6
0

Ɗan takarar gwamnan Jihar Sokoto a ƙarƙashin Jam’iyyar ADC, Hon. Manir Muhammad Dan Iya, ya bayyana matuƙar damuwarsa kan matakin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na zaɓar Farfesa Mustapha Aliu a matsayin Kwamishinan hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) mai wakiltar Shiyyar Arewa Maso Yamma.

Dan Iya ya buƙaci shugaban da ya sake duba wannan naɗi, tare da yin kira ga majalisar dattawa da ta binciki cancantarsa sosai kafin amincewa da shi, sakamakon kusancin dangantakar jini da ke tsakanin Farfesan da Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, da kuma shakku kan rashin nuna son kai a fannin siyasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here