Home Rahoto EFCC ta ayyana tsohuwar ministar Buhari, Sadiya Umar Farouq, a matsayin wadda...

EFCC ta ayyana tsohuwar ministar Buhari, Sadiya Umar Farouq, a matsayin wadda ake nema ruwa a jallo

10
0

DA DUMI-DUMI: EFCC ta ayyana tsohuwar ministar Buhari, Sadiya Umar Farouq, a matsayin wadda ake nema ruwa a jallo

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta ayyana tsohuwar Ministar Harkokin Jinƙai, Sadiya Umar Farouq, a matsayin wadda ake nema ruwa a jallo bisa zargin karkatar da kuɗaɗen gwamnati da kuma amfani da ofis ba daidai ba.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta, EFCC ta roƙi duk wanda ke da bayanin inda take da ya tuntuɓi ofisoshin hukumar ta lambobin da aka bayar.

Hukumar ta bayyana cewa Sadiya Umar Farouq mai shekaru 52 ’yar asalin Jihar Zamfara ce, kuma adireshinta na ƙarshe da aka sani shi ne EN008, Okpo River, kusa da titin Agulu a Maitama, Abuja.

Sadiya Umar Farouq ta riƙe muƙamin minista daga shekarar 2019 zuwa 2023 a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

EFCC na binciken ma’aikatar da ta jagoranta kan zargin badakalar kuɗi har Naira biliyan 37.

A ranar 16 ga Afrilu, 2026, babbar kotun tarayya ta Apo da ke Abuja ta bayar da sammacin kama ta, tare da Bashir Nura Alkali, babban sakatare na dindindin a ma’aikatar.

Alƙalin kotun, Jude Onwuegbuzie, ya bayar da umarnin ne bayan waɗanda ake tuhuma sun kasa bayyana a gaban kotu domin fara shari’arsu.

Sadiya Umar Farouq da Bashir Alkali tare da wani Sani Mohammed na fuskantar tuhume-tuhume guda 21 da suka haɗa da cin amanar aiki da amfani da ofis ba bisa ƙa’ida ba.

EFCC ta ce waɗanda ake tuhumar sun karkatar da kimanin dala miliyan 1.3 da kuma Naira miliyan 746.6.

A cewar hukumar, wani ɓangare na kuɗaɗen da aka mayar wa ma’aikatar daga shirin tallafin jama’a ne aka karkatar domin amfanin kai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here