Home Siyasa Atiku ya soki tsauraran sharuɗɗan beli da kotu ta sanya wa El-Rufai

Atiku ya soki tsauraran sharuɗɗan beli da kotu ta sanya wa El-Rufai

20
0

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya soki ƙin da Babbar Kotun Tarayya ta yi na sassauta sharuɗɗan belin tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, yana mai cewa sharuɗɗan sun yi tsauri matuƙa kuma suna da wahalar cikawa.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan hulɗa da jama’a, Phrank Shaibu, ya fitar a Abuja, Atiku ya ce irin waɗannan sharuɗɗa na iya zama wata hanya ta hukunta ‘yan adawa ta hanyar amfani da tsarin shari’a.

Ya bayyana cewa doka ta tanadi cewa wanda ake tuhuma ba shi da laifi har sai an tabbatar da laifinsa a kotu, yana mai cewa beli ya kamata ya kare wannan haƙƙi ba wai ya zama hanyar tsare mutum ba.

Atiku ya nuna damuwa kan sharadin da ya buƙaci El-Rufai ya gabatar da ma’aikacin gwamnatin tarayya mai mataki na 17 da ke da kadarori a Maitama ko Asokoro a Abuja, yana cewa irin waɗannan sharuɗɗa na da wahalar cikawa ga mafi yawan ‘yan Najeriya.

Ya kuma yi gargaɗin cewa irin wannan mataki na iya shafar sauran ‘yan ƙasa nan gaba, yana mai cewa adalci ya kamata ya kasance ba tare da son kai ko siyasa ba.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya buƙaci ɓangaren shari’a da ya tabbatar da cewa ana bai wa kowa adalci cikin gaskiya da adalci, yana mai jaddada cewa sharuɗɗan beli su kasance domin tabbatar da halartar wanda ake tuhuma a kotu, ba don ci gaba da tsare shi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here