Home Siyasa ADC ta ɗaurawa Tinubu Alhakin duk abin da ya Samu El-rufa’i

ADC ta ɗaurawa Tinubu Alhakin duk abin da ya Samu El-rufa’i

21
0

Ba zamu Yarda ba Idan wani Abu ya faru da El rufa’i kuma Tinubu ne zai ɗauki alhakin duk abin da ya faru da shi— ADC

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta yi gargaɗi cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne za a ɗora wa alhakin duk wani abu da ya faru da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, idan har wani abu ya same shi.

ADC ta bayyana hakan ne yayin da take nuna damuwa kan rahotannin da suka shafi tsare ko kuma yadda ake mu’amala da El-Rufai, tana mai cewa gwamnati ta tabbatar da an mutunta doka da kuma kare haƙƙin kowane ɗan ƙasa.

Jam’iyyar ta kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da aikinsu cikin adalci, ba tare da nuna son kai ko amfani da iko wajen murƙushe masu adawa da gwamnati ba.

ADC ta jaddada cewa kare rayuka da haƙƙin ‘yan ƙasa na daga cikin manyan alhakin gwamnati, tare da gargadin cewa duk wani abu da ya faru da El-Rufai zai jawo gwamnatin tarayya ta fuskanci tambayoyi daga ‘yan Najeriya da kuma ƙasashen duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here