Home Labarai Gwamnatin Oyo ta hana sayar da raguna a manyan tituna lokacin babbar...

Gwamnatin Oyo ta hana sayar da raguna a manyan tituna lokacin babbar Sallah

13
0

Gwamnatin jihar Oyo ta gargadi mazauna jihar da masu sayar da dabbobi da su guji sayar da shanu da raguna a manyan tituna yayin bikin Babbar Sallah mai zuwa.

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa, an bayyana hakan ne a taron masu ruwa da tsaki kan bin dokar hana kiwo a fili ta shekarar 2019 da aka gudanar a Ibadan.

Gwamnatin ta ce dokar ba ta da nufin muzgunawa wata ƙabila, inda ta bayyana cewa akwai kasuwannin da aka ware domin sayar da dabbobi a dukkan ƙananan hukumomin jihar.

Shugabar Hukumar Tabbatar da Bin Doka ta jihar, Mai shari’a Aderonke Aderemi mai ritaya, ta ce duk wanda aka kama yana sayar da dabbobi a kan manyan tituna zai fuskanci hukunci, yayin da za a ƙwace dabbobin da aka kama.

Ta ƙara da cewa dokar an samar da ita ne domin rage rikicin manoma da makiyaya, kare gonaki da kuma tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Haka kuma gwamnatin ta bukaci hadin kan jami’an tsaro, shugabannin al’umma, manoma da makiyaya wajen tabbatar da bin dokar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here