Ma’aikatan Hukumar Zakka da Waƙafi ta Jihar Katsina takwas sun yi hatsarin mota a hanyarsu ta zuwa Jihar Sokoto.
Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar, Malam Husain Kabir Yar’adua, ya fitar.
Ya ce, ma’aikatan sun gamu da hatsarin a tsakanin Yankara da Tsafe yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Sokoto domin halartar taron Bankin Raya Musulunci na Duniya IsDB.
Hukumar ta bayyana cewa mutum ɗaya ya samu karaya, yayin da sauran suka samu raunuka daban-daban, inda aka dawo da su Katsina kuma suke samun kulawar likitoci.
Hukumar ta bukaci al’ummar Musulmi da sauran jama’a su yi wa ma’aikatan addu’ar samun sauƙi.






