Home Rahoto Tinubu ya yi alƙawalin rage tsadar rayuwa, inganta tsaro da wutar lantarki...

Tinubu ya yi alƙawalin rage tsadar rayuwa, inganta tsaro da wutar lantarki bayan sake zaɓensa a 2027

7
0

Shugaba Tinubu Yace zan rage maku tsadar rayuwar da gwamnatina ta jefe ku a ciki zan kuma Inganta tsaro, samar da ingantacciyar wutar lantarki idan kun sake zaɓena a 2027 —Shugaba Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi alƙawarin rage tsadar rayuwa, inganta tsaro, samar da ingantacciyar wutar lantarki da kuma ƙara samar da ayyukan yi ga ‘yan Najeriya idan aka ci gaba da aiwatar da manufofin gwamnatinsa.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin gangamin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC a Jihar Jigawa, inda ya gabatar da abin da ya kira taswirar jam’iyyar na samar da ci gaba da wadata ga al’ummar Najeriya.

Shugaban ƙasar ya ce daga cikin abubuwan da gwamnatinsa za ta bai wa muhimmanci akwai kare rayukan jama’a, inganta harkokin kiwon lafiya da samar da damammaki a kowace ƙaramar hukuma ta ƙasar.

“Za mu rage tsadar rayuwa, mu inganta tsaro, sannan mu samar da ingantacciyar wutar lantarki ga ‘yan Najeriya. Ba irin tsohon tsarin mayar da harkar wutar lantarki hannun kamfanoni masu zaman kansu wanda bai yi aiki yadda ya kamata ba,” in ji Tinubu.

Ya kuma yi alƙawarin bunƙasa masana’antu, tallafa wa ƙananan da matsakaitan ‘yan kasuwa, tare da faɗaɗa damammakin samun ayyukan yi, musamman ga mazauna yankunan karkara.

Tinubu ya bayyana cewa waɗannan shirye-shirye na daga cikin muhimman manufofin da gwamnatinsa ke son aiwatarwa domin inganta tattalin arziki da sauƙaƙa wa jama’a matsalolin rayuwa.

Alƙawuran na zuwa ne yayin da jam’iyyun siyasa ke ƙara zafafa shirye-shiryen neman goyon bayan ‘yan Najeriya gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here