Dubban matasa sun nuna goyon bayansu ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Sakkwato Alhaji Ahmad Aliyu Sokoto domin ganin sun samu nasara a zaɓen 2027 in da suke neman zaton na biyu.
Wannan yunƙurin masu ya haɗa ɗimbin magoya baya da kodinetocin matasa a ƙananan hukumomi 23 na jihar wannan motsawar za ta ƙara bunƙasa tafiyar shugaban ƙasa da Gwamna a tsakanin matasa.
Gangamin wanda Honarabul Nasiru Bazza ya jagoranta tare da jagororin matasa a dukkan ƙananan hukumomin jihar don bayyana goyon bayansu ga jagororin guda biyu.
Zagayen da ya karaɗe dukkan birnin jihar Sakkwato an yi tarukan siyasa da ɗaga kwalaye na nuna goyon baya ga jam’iyar APC da Tinubu da Ahmad Aliyu tare da rera waƙoƙin jinjina.
Bazza a lokacin da yake jawabi ga mahalarta ya nuna gamsuwarsa ga mulkin shugaban ƙasa Tinubu da Gwamna Ahmed Aliyu kan haka matasa suka yi wannan hoɓɓasar don tabbatar da ɗorewar gwamnatin tarayya da jiha baki ɗaya.
Ya ce goyon bayan jagororin biyu samar da cigaba ne ga ɗorewar gwamnati domin shiraruwan da aka ɗauko su ɗaure ba yanke wa a Nijeriya musamman a Sakkwato.
Bazza ya haƙiƙance matasa aiyukkansu ya sha gaban goyon baya kawai su ƙashin bayan dimokuraɗiyya ne suna da ƙarfi da basirar sauya kalar siyasa a ƙasar nan.



