INEC ta hana jam’iyyar NDC Code lambar na ɗora sunayen ‘yan takara a shafin Hukumar.
Jam’iyyar National Democratic Coalition (NDC) ta zargi Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da kin ba ta lambar shiga (access code) da ake buƙata domin ɗora sunayen ‘yan takararta a tsarin rajistar ‘yan takara na hukumar.
Zargin na zuwa ne bayan wata Babbar Kotun Tarayya ta umarci INEC da ta soke rajistar jam’iyyar NDC, hukuncin da ya haifar da ce-ce-ku-ce kan matsayin jam’iyyar a doka da kuma makomarta a zaɓe masu zuwa.
Da yake magana kan lamarin, Sakataren Yaɗa Labarai na ƙasa na jam’iyyar, Osa Director, ya ce NDC ta tuntubi INEC domin samun lambar shiga da za ta ba ta damar kammala ɗora sunayen ‘yan takararta, amma hakan bai samu ba.
A cewarsa, jami’an INEC sun shaida musu cewa za su sake tuntubar su daga baya, lamarin da ya hana jam’iyyar kammala aikin kafin umarnin kotun na soke rajistarta.






