Home Siyasa Matsalar tsaro: Akwai buƙatar Gwamnonin Arewa su zauna da Shugaban ƙasa don...

Matsalar tsaro: Akwai buƙatar Gwamnonin Arewa su zauna da Shugaban ƙasa don kyautata danganta da Nijar—–Dasuki

22
0

Honarabul Abdulsamad Ibrahim Dasuki ɗan majalisar waƙillan Nijeriya da ke waƙiltar Tambuwal da Keɓɓe ya nemi gwamnonin Arewa su zauna da Shugaban ƙasa Bola Tinubu su gaya masa buƙatar da ake da ita na  kyautata dangantaka tsakanin Nijar da Arewa ganin yanda harkar tsaro ta ƙara taɓarɓarewa a garuruwan da ke iyaka da ƙasar Nijar.

Honarabul Dasuki ya yi kalaman ne a hidikwatar jam’iyyar ADC dake Sakkwato bayan ya  karɓi karrama wa da shugabannin ƙananan hukumomin da yake waƙilta suka yi masa kan zama mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar waƙillai da ya yi.


“Rashin tsaron nan kowa ya san abin da ke faruwa a Gabasci da kudancin Sakkwato mutanen Fakku, Sabon Birni da sauran wurare suna cikin matsalar yakamata a ɗauki mataki gaskiya gwamnatin tarayya da jihohi sun kasa, ba mu ga an ɗauki wani mataki na gyara ba.”


“Ina baiwa Gwamnan Sakkwato shawara kan tsaro a harkar ‘yan sandan daji, ya ga shugaban ƙasa domin a ba shi dama shi ma kamar yanda aka baiwa Oyo da Katsina, don anan ma akawai matsala ‘yan bindigar daji.”

Kan maganar samar ‘yan sandan jihar ya ce sun san muhimmancin harkar tsaro ya sa suka yarda  a samar da ɗan sanda jiha a majalisar waƙillai domin ba a siyasantar da harkar tsaro.


Ya ƙara da cewar a 2027 zaɓe kan jam’iyyar su ADC za ta yi nasara da ikon Allah, amma akwai buƙatar a wayar da kan jama’a kan matsalar sake zaɓar gwamnatin APC.Ya nanata cewa yakamata a ce mafi ƙarancin albashi dubu 150 ne  a Sakkwato  riƙa baiwa ma’aikata domin akwai kuɗin da za a yi haka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here