Bangaren PDP na Kabiru Turaki a jahar Kebbi sun amince su marawa Gwamna Nasir Idris baya a zaɓen 2027
Bangaren jam’iyyar PDP na Kabiru Turaki a Jihar Kebbi ya amince da marawa ɗan takarar jam’iyyar APC kuma Gwamnan Jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu, baya a zaɓen gwamna na shekarar 2027.
An cimma wannan matsaya ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar ƙarƙashin jagorancin tsohon Minista, Buhari Bala, da Janar Ishaya Bamaiyi, inda aka tattauna kan makomar jam’iyyar a jihar da kuma matakan da ya kamata a ɗauka gabanin zaɓen 2027.






