Home Siyasa Ba dukkan jihohin Nijeriya Tinubu zai tafi yaƙin neman zaɓen 2027 ba

Ba dukkan jihohin Nijeriya Tinubu zai tafi yaƙin neman zaɓen 2027 ba

5
0

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce ba zai iya raka mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC zuwa dukkan wuraren da za su gudanar da kamfen gabanin zaɓen 2027 ba.

Tinubu ya ce akwai abubuwan da suke buƙatar ya mayar da hankali kan gudanar da su a lokacin da ake yawon kamfe din.

Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Abuja, yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC, inda ya buƙaci mambobinsa su kai saƙon jam’iyyar ga ƴan Najeriya a faɗin jihohi da ƙananan hukumomi.

Shugaban ya ce ya amince da shawarar cewa bai kamata yaƙin neman zaɓe su ɗauke masa hankali daga gudanar da mulki ba, yana mai cewa Najeriya na buƙatar kulawarsa a halin yanzu.

“Kun gargaɗe ni da kada wahalhalun yaƙin neman zaɓe su ɗauke min hankali daga gudanar da mulki, kuma na amince da wannan shawara. Najeriya na buƙatar kulawa sosai a yanzu,” in ji shi.

Tinubu ya buƙaci mambobin kwamitin su fahimci cewa ba zai iya kasancewa tare da su a dukkan wuraren da za su gudanar da kamfen ba, saboda gwamnati na da wasu kuɗaɗen da za ta biya da kuma wajibai na kuɗi ga ƙasashen waje.

Ya ce: “Don haka, ku yi haƙuri idan ba zan iya zuwa ko’ina tare da ku ba. Muna da kuɗaɗen da za mu biya, kuma masu bin mu bashi daga Amurka ba za su jira ba.”

Shugaban ya kuma ce gwamnatinsa na buƙatar jawo hankalin masu zuba jari da za su zuba kuɗaɗensu a Najeriya na dogon lokaci domin samar da kyakkyawar makoma ga ’ya’yan ƙasar.

Ya ce yana son masu zuba jarin su zo Najeriya su zauna, su kuma zuba jari domin amfanin al’umma da kuma makomar yara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here