Home Siyasa In har Tinubu ya faɗi a jihar ka, ba za ka yi...

In har Tinubu ya faɗi a jihar ka, ba za ka yi mana kuri ba in ya lashe zaɓe—-Wike ga Gwamnonin APC

110
0

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya gargaɗi gwamnonin jam’iyyar APC da sauran mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar da kada su yi ikirarin nasara a zaɓen 2027 idan ba su samu nasarar kayar da abokan hamayya a jihohinsu ba.

Wike ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a Abuja, inda aka naɗa shi mai kula da yaƙin neman zaɓe a Abuja da Jihar Rivers.

Ya ce babban aikin kowane mamba a kwamitin shi ne tabbatar da sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu, ba tare da la’akari da matsayin da yake da shi a cikin kwamitin ba.

“Idan ba ku kai wa shugaban ƙasa nasara a jihohinku ba, ko da ya yi nasara, kada ku ce mun yi nasara,” in ji Wike.

Ya ƙara da cewa ya shaida wa shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa cewa idan Tinubu bai yi nasara a Legas ba, bai kamata a ce an yi nasara ba.

Wike ya kuma yi alƙawarin cewa za su yi ƙoƙarin ganin Tinubu ya samu gagarumar nasara a Rivers da Abuja a zaɓen mai zuwa.

Ministan ya yaba wa gwamnonin Anambra da Osun, Chukwuma Soludo da Ademola Adeleke, bisa halartar taron, yana mai cewa hakan ya nuna irin goyon bayan da Tinubu ke samu gabanin zaɓen 2027.

Haka kuma, Wike ya kare gwamnatin Tinubu, yana mai cewa gwamnatocin baya sun san matsalolin ƙasar amma sun gaza samar da mafita.

Da yake magana kan matsayinsa a jam’iyyar PDP, Wike ya bayyana kansa a matsayin jagoran jam’iyyar, yana mai cewa babu jagorori biyu a PDP.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here