Home Daga Marubutanmu Ƙaddara Ta Riga Fata: Fita Ta Bakwai

Ƙaddara Ta Riga Fata: Fita Ta Bakwai

2
0

AUNTY NICE✍🏼
@wattpad AuntyNice.

SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI

SHAFI NA 7📑

__📖 Tun da muka shigo compound ɗin gidan mu ido na ya sauka a side ɗin Dr Hussain, gaba na sai faɗuwa ya ke yi, domin hango motan shi a parking lot ɗin gidan, wanda daga motan shi ne sai na David, daga dukkan alama sune suke gidan, don nasan Peter ba sosai ya cika zaman gida ba.

Hannun Amal na riƙe, ɗayan hannu na kuma ina riƙe da jakan kayan ta, duk na rasa samun nutsuwa a zuciya ta sai faɗuwar gaba na ke ji, a haka har muka ƙara sa na buɗe ƙofan gidan mu ka shiga.

Muna shiga parlon Amal ta kwanta tana ta ya mutsa fuskan ta, ni kuma na wuce ɗaki na kai mata kayan ta, cikin parlor na dawo na zauna a gefen ta ina duban ta da tausayi.

Miƙo ƙafan ta tayi in da na ke ta ce, “don Allah Sister danna mun ƙafa ta, duk ciwo suke mun”.
ta faɗa kaman zata zubar da hawaye.

Tausayi ta bani na ta shi da sauri na fara daddana mata ƙafafun ta, sai nishi ta ke yi, muna cikin haka wayan ta ya fara ringing, (Ammi na) na gani yana yawo a kan screen ɗin wayan, da sauri na bar abinda na ke na miƙa mata wayan, abin tausayi da ƙyar ta ta shi zaune ta ɗauki wayan, bayan sun ɗanyi magana da Ammin ta, sai Abbun ta ya karɓi wayan shi ma suka yi magana, can sai ta miƙo mun wayan, ina karɓa Abbun ta yace mun,

“Humaira na gode da ɗawainiya ko, idan kin ga jikin zai tsanan ta ki kira number Dr’n ta don Allah, yanzu zan kira shi na sanar mishi, za ki ga Dr Abdallah a contact ɗin ta, duk yadda ake ciki ki sanar mana, mun gode da ƙoƙarin ki, Allah ya miki albarka”.

Ina a jiye wayan na dube ta da alaman ta na son yin bacci, a hankali nace, “Sister me zan dafa miki?”.

Da ƙyar ta buɗe idon ta, girgiza mun kai ta yi alaman a’a bata son komai, bance mata komai ba na ci gaba da daddana mata ƙafan, har sai da naga bacci ya ɗauke ta, sannan na miƙe naje kitchen na ɗaura faten dankali, sannan na gyara ganye alayyahu mai yawa na ajiye a gefe.

Ina fitowa parlor na ƙura mata ido, ganin bacci ya ɗauke ta babu yadda zanyi na ta she ta ta yi sallah ina tsoron ciwon na ta, ga shi kuma lokacin sallan magrib ya gaba to, haka na wuce ɗaki na ɗauro alwala nayi sallah, bayan na idar da azkhar na wuce kitchen na zuba wadataccen ganye na, sannan na ɗauko apple guda huɗu na wanke su, na yanka na zuba a blander nayi blanding ɗin su, saboda ina ji ana cewa yana amfani a jikin masu ciwon sickler, a fridge na ajiye sannan na sauke abincin na juye a cikin cooler na kai su kan dinning.

Ina fitowa da komai na dawo gefen ta na zauna na ƙura mata ido, har lokacin sallan isha ta yi ba ta ta shi ba, bayan na idar da sallah ne na fito nazo na same ta tana zaune dirshan a ƙasa ta mimmiƙe ƙafan ta a ƙasa tana ta ya mutsa fuskan ta.

Da sauri na ƙaraso in da take ina duban ta nace, “ya fara miki ciwo ne? Ko zaki iya ta shi ki yi sallah?”.

Bata ce mun komai ba ta miƙo mun hannu alaman na taimaka mata ta tashi, da sauri na saka hannu na miƙa mata, ta na tashi muka wuce har toilet ɗin ɗaki na, sannan na barta ta shiga ta ɗauro alwala, tana fitowa na shimfiɗa mata sallaya, abin tausayi a zaune tayi sallan kaman za tayi kuka har ta idar.

Jingina kanta ta yi a jikin gado tana ɗan shirin komawa bacci, gefen ta na zauna nayi ta lallaɓa ta a kan taci abinci, da ƙyar ta yarda, haka naje na zuba mata abincin a plet na kawo mata har ɗakin, ɗayan hannun kuma ina ɗauke da ƙaramin jug dana zuba taceccen ruwan apple ɗin a ciki.

Duk yadda ta so taƙi cin abincin ban barta ba, sai dana takura ta ta cinye abincin, sannan na miƙo mata magungunan ta tasha, tana gamawa Abbun ta ya kira wayan ta, ni na ɗauki wayan muka gaisa, tambaya na jikin ta ya yi cikin damuwa da nuna kulawan su a kanta da ciwon ta.

“Humaira kina ga zaku iya kwana a gida ko kuma Dr’n ta yazo ya tafi da ita hospital”?.

“Abbu babu komai, zamu iya kwana, yanzu ma ta samu ta yi bacci, bayan ta tashi ne tayi sallah kuma taci abinci, yanzu ma tasha drugs ɗin ta, ina ga babu komai insha’Allahu, don naga kaman ya fara mata sauƙi”.

Bayan mun gama wayan ne na wuce parlor domin naci abincin, da ya ke ban yi mai yawa ba, duka na juye a plet ɗin sannan na zauna na fara ci, amma gaba ɗaya zuciya na ya kaso kashi biyu, ɗaya ina tunanin ya ya zamu yi ni da Amal idan ciwon ya tashi cikin dare? Ɗayan zuciyan kuma ina tunanin Dr Hussain da Dr Khadija dana gan su tare, ko yanzun ma tare suke ita da shi ko kuma ya ya abin yake? Haka dai nayi ta hira da zuciya ta har na gama cin abincin.

Books ɗina na baje su a parlon ina karatu, bayan na duba Amal na ga tayi bacci.

Bani na tashi ba sai around 11:00 pm, ina shiga ɗakin na duba ta naga still baccin ta ta keyi, a hankali kada na tashe ta na wuce toilet domin nayi wanka.

Ina fitowa a toilet na ɗauki turare na mai sanyin daɗi na shafe jiki na da shi, sannan na ɗauko wando da riga masu ɗan kauri kaɗan na saka, domin gaba ɗaya yau naji garin kaman da ɗan sanyi, hula na saka na ɗale gadon, bayan nayi addu’a na shafa na kashe mana wutan na kwanta.

Kaman a cikin mafarki na ke jin nishin mutum a kusa dani, a firgice na tashi zaune na kunna wutan ɗakin na juya inda Amal ta ke, abin tsoro ita ɗin ce kuwa zaune ta riƙe cikin ta ta na ta nishi, da sauri na matso kusa da ita na rungume ta, ido na cike da hawaye ina tambayan ta,

“Sister ina yake miki ciwo? Ko na kira Dr ne”?.

Ta riƙe ni da ƙarfi duk idon ta sun yi fari ƙal na alaman babu jini, tana nishi hannunta riƙe da cikin ta ta ɗaga mun kanta alaman na ƙira shi.

Da sauri na jawo wayan ta da yake kan bedside na buɗe, inda naga 2 misscall ɗin Abbun ta, amma ban bi takan shi ba na danna ƙiran Dr Abdallah, bai fi ringin biyu ba ya ɗauka bakin shi ɗauke da sallama, jiki na yana rawa na ce.

“Hello Dr Amal ce..” na faɗa kaman wanda aka ƙwaci sunan a baki na, a cikin nutsuwa yace mun, “in da ku ke a kwai abin hawa ne? Ko kuma nazo na ɗauke ta za ki bani address”?

Ta shi na yi tsaye na ce, “ka zo don Allah”.

sannan na ba shi address ɗi na, da sauri na shiga toilet ɗin nayi fitsari kuma nayi brush, ina fitowa na buɗe sif ɗina na ɗauko wani after dress na ɗaura akan kayan baccin sannan nayi rolling ɗan gyalen a kaina, jaka na na jawo na jefa carbi na da waya ta, na riƙo Amal muka ta shi tsaye ina kallon ta nace, “sister za ki shiga toilet”?

Ɗaga mun kai tayi alaman zata je, da sauri na kai ta, da ƙyar ta na kuka zuwa lokacin ta yi fitsari, tana ta shi ta yi alwala da ƙyar, na saka hannu na riƙo ta muka fito parlor.

Na lura kullum Amal a cikin alwala ta ke, yau ɗaya na ji ta burgeni wato duk zafin ciwon da ta ke ji bai hana ta yin alwalan da ta saba ba ko? Ya Allah nima ka bani ikon yin shi a rayuwa ta, muna zama bamu daɗe ba naji an buɗe gate ɗin mu, motan Dr ta shigo, kafin na yunƙura sai jin wayar ta ta fara ringing, ban tsaya ɗaukan wayan ba, na kama hannun ta muka yi hanyar fita waje.

Muna fitowa na tsaya rufe ƙofan sai ga Dr Abdallah da sauri ya fito a motan shi ya ƙara so in da mu ke, dai-dai lokacin na ga Dr Hussain ma ya buɗe ƙofan shi yana tsaye yana kallon mu.

Amal ta kasa ɗaga ƙafan ta ta yi tafiya sai kuka ta ke yi, ganin haka na yi sauri zan riƙe ta, amma sai Dr yace a’a ki riƙe bag ɗin ki bari na taimaka miki, kallon shi na yi kaɗan na juya kaina gefe a zuciya ta ina cewa ashe ma Balarabe ne shima Dr.

Ban san lokacin dana juya na kalli Dr Hussain ba, wanda har lokacin yana tsaye yana kallon mu, jikin shi ɗauke da wasu kayan bacci masu masifar kyau green colour, alaman bazai ce mun uffan ba, sai nima na daure na bi bayan su Amal, a lokacin David da Peter suka fito, ganin mune zamu fita naga sun ƙara so in da muke da sauri.

“Preety bata da lafiya ne?”.
Peter da ke ƙarasowa kusa da ni ya tambaye ni, cikin damuwa na ke gaya mishi ita sickeler ce kuma ta samu crises tun jiya da yamma, yana bin mu da kallon tausayi, sai David ya jeho mun tambayan.

“Preety why baki kira mu mun taimaka muku zuwa hospital ba? Naga kin nemo wani da ga wani wuri bayan muna tare kin kuma san akwai abin hawa?”.
Ya faɗa yana duban Dr Abdallah daya buɗe bayan motan ya kwantar da Amal.

Kafin nace komai, sai Dr Abdallah ya ɗa go kan shi da murmushi yana miƙawa David hannu kuma yana gaya mishi yayi haƙuri bawai mun nemo shi daga wani wuri ba ne, dama shi Dr’n Amal ne.

Bayan sun tambaye shi asibitin da zamu je ya gaya musu, ni kuma na buɗe gaban motan na shiga, ko tayar da motan ba’ayi ba kawai naji an buɗe in da na ke zaune, sai jin muryan shi nayi ya na cewa.

“koma back seet in da ta ke ki zauna”.
ban iya mishi musu ba jiki na yana rawa na fita na koma bayan, sannan shi kuma ina ganin shi ya shige ya zauna, idon shi a kan Dr Abdallah sannan ya ce mishi.

“Aisha Sister na ne”.
Dr Abdallah bai ce komai ba sai smilling da ya yi ya ja motan da sauri muka tafi.

Tun da mu ka shiga motan babu abinda ka ke ji sai sautin kukan Amal, ga wani miƙewa da ta ke ta yi, muna isa Dr Abdallah ya fito da sauri ya buɗe motan, lokacin kuma wasu nurses sun turo ɗan gadon su na ɗaukan marasa lafiya suka ɗauke ta, cikin gudu-gudu muka bi su ni da Dr Hussain, emargency room Dr ya wuce da ita, bamu daɗe ba wasu Drs guda uku suka bi bayan shi ɗaya namiji biyu kuma mata.

A reception ɗin asibitin muka zauna ni da Dr Hussain, babu wanda ya kula wani a cikin mu, har tsawon wasu mintu na, sai ga Dr Abdallah ya fito hannun shi riƙe da waya, da ga dukkan alamu shi da Abbun Amal suke wayan, har in da muke zaune ya zo ya tsaya ya kuma cigaba da wayen shi haka zalika idon shi a sauke a kaina ya ƙura mun ido yana amsa wayan.

Suna gama wayan ya dube ni da murmushin dana lura kaman baya barin fuskan shi, murya a nutse da ya nuna yanayin maganan shi ke nan ya dube ni yace,

“ƙawar ki mun samu tayi bacci, pain ɗin ya ɗan mata sauƙi, amma kuma tana buƙatan ƙarin jini, shi ne muke magana da Abbun ta”.
ya faɗa har lokacin fuskan shi ɗauke da murmushi yana duba na.

“Da ka ke mata bayanin abinda zaka yi to ita mai ta sani a game da aikin ka? Ina ce kun gama magana da mahaifin yarinya? Ina ga kaman ba lallai bane sai kazo ka mata bayani kawai ka aiwatar da abinda ya ke aikin kane”.

Dr Hussain ya faɗa fuskan shi a matuƙar ɗaure, wanda sai da naji kunyar abinda ya faɗa, amma abin mamaki Dr Abdallah juyawa yayi yana duban shi fuskan shi har lokacin ɗauke da murmushi.

Shi kuma Dr Hussain kawar da kai yayi gefe kaman bai lura da kallon shi Dr Abdallah ya ke yi ba, “Yayan mu kada ka samu damuwa da magana na, kasancewar ta re su ke ciwon ya tashi, kuma naga ita ƴar’uwarka irin damuwan da ta shiga shiya sa na mata baya ni don hankalin ta ya kwanta, don ɗazu da muka yi waya na jita cikin yanayin damuwa”.

ya faɗa ya na duba na kaman wanda ya ke son fahimtan wani abu a tattare dani.

Bai jira mai Dr Hussain zai ce ba ya juya ya koma in da ya fito, muna zaune shiru babu mai cewa uffan sai wucewar mutane kawai ta gaban mu kaman safiya da ce ta yi, daga dukkan alamu asibitin na manya mutane ne, kuma babban asibiti ne.

“Wa to ke har wani kiran wayan shi ki ke yi ko? To kiyi deleting number’n tun da dai an kawo ta asibitin”.
Dr Hussain ya faɗa yana bina da harara.

Fuska na a tsuke na dube shi sannan nace, “ni fa babu number’n shi a waya na, dama ta wayan Amal Abbun ta yace na kira shi idan jikin ya ƙi…..”.

Ban ƙarasa faɗar abunda ke baki na ba, na ji yayi tsaki ƙasa-ƙasa, sannan ya ɗan dube ni ya ɗa ga kafaɗa alaman babu abinda ya dame shi, ganin hakan da ya yi sai na ji raina ya ɓaci, tashi nayi zan bar wurin, kawai sai na ji yace,

“Meye ya ke damun ta?”.
Dr Hussain ya tambaye ni.

“Sickler ce”. na bashi amsa a taƙaice.

Zaro ido yayi yana kallo na a razane, can kuma sai yace, “shi ne kuma kika ɗauke ta zuwa yawo bayan kinsan ciwon su baya son wahala?”.

Zunɓuro baki na yi ina hararan shi ƙasa-ƙasa ina ɗan ƙunƙuni na.

Ya na kallo na yace, “zagi na ki ke yi Aisha?”.

Ina kallon shi kaman zan yi kuka na ce,
“ni meye zai sa na zage ka? Kawai cewa na yi kaima ai yawo ka je kaida matar ka, kuma kaƙi kula ni da ka ga tana gun, bayan ka tafi ka daɗe baka dawo ba, ko zuwa duba ya ya na ke ba ka yi ba saboda kana wurin matar ka”.

na faɗa kaman zan zubar da hawaye.

Kallo na ya tsaya yana yi kaman yaga sabon abu, amma abin mamaki ko bin ta magana ta bai yi ba kawai sai na ji yana tambaya na, “Meye gyenotype ɗin ki?”.

Turo baki na yi ina duban shi kaman zan zunduma ihun haushi, bansan lokacin dana harare shi ba, na kaɗa kaina nace,

“meye problem ɗin ka da sanin gyenotype ɗi na? Ina ce kasan na koɗaɗɗiyar matar ka”.
Na faɗa ina tashi tsaye zan bar wurin.

“Ka da ki yadda ki bar nan wurin, kuma ki shirya yanzu zamu koma gida, don asibitin nan ba a kwana, yana fitowa muka ji ya ya ta ke, zamu ta fi gida”.

ya faɗa idon shi tsaye a kaina, zuciyar shi kuma yana tuna wani lokaci kusan irin haka, lokacin yana service a central bank branch ɗin su da ke bauchi, sun shigo gida da wasu corpers ƴan’uwan shi, amma har da mata a cikin su, suna tafiya ya ce Aisha ta kawo mishi abinci, amma firr yarinyar nan ta dinga mishi tsiwa kaman ba ita ba,

“Yayan mu to me ya sa ba ka ce wa ƴan matan ka su kawo maka ba? Ni sai kawai ka dinga zuwa da ƴan matan ka suna yiwa mutane kallon banza kaman sun ga sa’o’in su, ni wallahi suka sake zuwa sakawa zanyi a ɗaura maka aure da figaggiyar ciki, idan yaso ka samu mai kawo maka abinci”.

Aisha ya tuna yadda ta mishi ranan, babu ko ɗigon tsoron shi a idon ta, gashi yau ma Humaira ta sa ke maimaitawa.

Yana kallo na bai ce uffan ba, ni kuma sai harare-harare na ke yi, can jumawa yayi ɗan murmushi yana duba na ya ce,

“Ko ta burge kine matar tawa?”.
Ya faɗa yana jiran ya ji wani irin amsan zan bashi, ko zai zo ɗaya da na Aisha a wancan lokacin.

Juyowa nayi da sauri na kalle shi fuska a ɗaure nace,

“kai ka ke ganin kyawun ta tun da ka na son ta, ni dai nasan ko kusa ba za’a haɗa ta da ni ba wurin kyau, bari kuma kaga lokacin da nawa masoyin zai iso, za ka ji ya tabbatar maka da samun irin mai kyauna sai an tona”.

na faɗa ina girgiza jiki na ina fari da ido na.

Miƙewa yayi tsaye yana duba na da mamaki, domin lokacin da Aisha ta gama mishi wannan mitan duban ta yayi yace, ” Sister Aisha ko dai Blessing ta burge kine? Halan kema kyaunta ya burge ki”?

Harara Aisha ta mishi a wanchan lokacin sannan ta dube shi tace, ” kai kaga kyaunta don ka na sonta, amma ni ko ku sa dani a ka kawota wallahi zan dushasheta, kuma ka jira ranan da zan fara samari zaka ji an faɗa maka haka”.

ta faɗa tana wucewa parlon Ummi a lokacin, shi kuma yayi murmushi ya wuce side ɗin su da Hassan.

Duban fuska na ya tsaya yana yi, har Dr Abdallah suka fito daga ɗakin, wasu nurses biyu mata suna gangaro Amal a gado tana bacci, hannun ta ɗauke da ledan jini, zuwa in da suke na yi na tsaya ina kallon ta.

Suna shiga wani ɗaki mu ka bi bayan su har da Dr Hussain, bayan an kwantar da ita ne nurses ɗin ɗaya ta fita ɗaya kuma ta nemi wuri ta zauna, Dr Abdallah yana duba na da murmushi ɗauke a fuskar shi yace,

“Ƴan mata Alhamdulillahi mun samu jinin da ya yi dai-dai da nata, kinga har ta samu ta yi bacci, yanzu za ki iya komawa gida sai wurin 8:00am za ki iya zuwa ki duba ta”.
ya faɗa ya na ƙura mun idon shi.

Kallon shi na yi a marairaice nace, “Plz Dr kabar ni na kwana ina ganin ta mana, kaga asuba ma ya kusa”.
Na faɗa ido na yana cikowa da ƙwalla.

Hannun Dr Hussain na ji ya kamo nawa a hankali na ji yana cewa,

“kibar su suyi aikin su mana Aisha, Kizo mu koma da safe zan dawo da ke insha’Allahu”.

na buɗe ba ki zan yi mishi musu, sai na ga ya lumshe ido ya buɗe yana juya mun kanshi alaman baya son musu.

Bance komai ba na bishi yadda yake jana muka fita a ɗakin, ni kuma ina ta waiwayen Amal da ke bacci kaman zanyi kuka, amma haka Dr Hussain ya jani muka fita, shi kuma Dr Abdallah sai bin mu yake da murmushi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here