Home Daga Marubutanmu ƘADDARA TA RIGA FATA

ƘADDARA TA RIGA FATA

9
0

°°ƘADDARA TA RIGA FATA°

NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NICE
@wattpad AuntyNice.

SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI

SHAFI NA 6

__ Nafi awa ɗaya a tsugune a wurin ina kuka, don ina jin hayaniyar sauran ƴan gidan da suka fito suka bawa Dr haƙuri, kuma nayi tunanin ko sun ɗauka laifi nai mishi yasa yazo yake masifan na buɗe ƙofan, a hankali na tashi na hau kan gado na, wata zuciyar ta bani shawarar na gayawa Daddy, amma wata zuciyar tana kwaɓa na da cewa,

“ke Humaira Daddy’n ki yana sanin abinda ya faru zai zo ya canja miki gida ko kuma ma ya canja miki school, kuma daga wannan ranar zai zamo kin daina ganin Dr ki”.

Ɗan juyawa gefe ɗaya nayi har lokacin ido na bai daina zubar da hawaye ba, a fili na furta,
“Dr’n mu me ya sa ka ke mun kallon wata ce? Nifa wallahi Humaira ce ba Aisha ba”.
na faɗa hawayen ya na ƙara bin fuska na.

Da ƙyar na ta shi nayi sallar azahar na sake komawa gado na kwanta, haka la’asar ta same ni, shima tashi nayi na sake hawa gado, banfi ƴan mintuna ba Daddy ya ƙirani, jiki na har rawa yake don fargaban ko zai gane murya na nayi kuka, ina ɗauka a sanyaye na ce.

“Hello Daddy na”.
sannan na yi shiru ina jin bayanin da ya ke mun cikin mamaki.

“Sweet heart jiya wani lecturer ɗin ku ya ƙira ni, sunan shi Dr Hussain ya gaya mun shine yake gefen gidan ki wanda na ce miki mai shi baya nan ne lokacin da mu ka zo, amma ance mun a kwai mutum a gidan, ya gaya mun kin fito za kije school kika yar da wayan ki a ƙofan gida shine ya ɗauki number na, mun gaisa ya gaya mun kina ƙoƙari a school sannan kina kula da tarbiyan da na baki, sannan idan na amince zai dinga miki extra lesson a gida”.

Rufe ido na nayi hawaye yana bin fuska na, wanda ni kaina bansan dalilin shi ba, can naji muryan Daddy yana cewa.

“Kin amince da yanayin shi da kuma mutuncin shi? Ko kuma na ba shi haƙuri? Don ni naji daɗi da ya iya gaya mun kanshi da kuma niyyan shi, kuma daga dukkan alamu ba yaro bane, don ban ji rawan kai a Maganan shi ba, amma ke me kika gani? Saboda shi mugu baida kama, kullum ina gaya miki”.

“Daddy ba yaro bane, kuma ina ga ma kaman yana da family shima, aka sari ma yana yawan mun faɗa ko idan na fito da ƙaramar riga, kuma babu shirme a al’amuran shi ko kaɗan Daddy, ni dai ta wuri na ba bu komai, umurnin ka nake jira”.

“Ba bu komai sweet heart, sai dai zan ja miki kunne ki kula da tarbiyan ki da kuma mutuncin ki a duk inda ki ka samu kan ki, ki kuma tuna rayuwar mace da na namiji a kwai ban-banci, Allah ya miki albarka”.

Bayan munyi sallama da Daddy na ta shi na shiga na sake wanka, ɗauko jaka na nayi da niyyan na yi karatu amma abu ya gagare ni, a hankali na fita zuwa parlor na, na daɗe a tsaye ina jayayya da zuciya ta, shin na leƙa Dr ne ko kuma na bari, kada naje bai huce ba ya sake rarako ni.

Zuwa wani lokaci dai na haƙura na daure, ina zuwa bakin ƙofan shi zan fara knocking sai ɗaya daga cikin ƴan gidan mu mai suna Peter ya fito daga na shi gidan, yana ɗan murmushi ya ƙaraso inda na ke tsaye, yana kallo na da dariya kaɗan a fuskan shi yace.

“Preety me ya faru naga kina gudu Oga kuma ya biyo ki ran shi a ɓace? Any way ba sai nasan me ya faru ba, don nasan almost shekaru uku muna tare da shi anan, ban taɓa ganin yayi faɗa da kowa ba, babu ma mai zuwa gidan shi idan ba ke dana fara gani kin shiga ba, gashi kin saka naga ɓacin ran shi sosai ɗa zu, don na ba shi haƙuri amma naga ya fita a motan shi ran shi a ɓace”.

Yana gama bayanin shi naji raina ya ɓaci, wato Dr yayi fushi ne shiya sa ya bar mun gidan? Hala ma wurin matar shi ya tafi domin ta kwantar mishi da hankali, ni kuma zuciya ta ta fashe ni ka ɗai ko? Hmmm dawo da kallo na nayi kan Peter ina murmushi, domin bana son ya fahimci wani abu, ina kallon shi nace.

“kasan shi cousin ɗina ne, so baya son yaga bana karatu, shi yasa ɗazu dana ce ni zanje na kwanta ne ba lokacin zanyi ba shi ne ran shi ya ɓaci, ni kuma na gudu ne ka da ya saka ni yi dole”.
na faɗa ina ƙara murmushin fuska na.

Shima murmushin ya yi ya na ƙara gyara tsayuwar shi, yana duban cikin ido na yace,

“gaskiya preety baki kyauta ba, ai duk wanda ya ke so ka yi karatu shi mai son ka ne, kinga gaskiya ki daure kiyi karatu idan kina so ku shirya da brother’n ki, kinga shi mayen karatu ne fa”.

Ya ƙara sa faɗa ya na juyawa da dariya a fuskan shi.

Ganin ya juya nima na koma nawa side ɗin zuciya ta cike da tunanin me yasa ran shi zai ɓaci irin haka? Nifa na gaya mishi gaskiya bani bace Aishan amma yaƙi yadda, to ko dai yana da wani problem ne a brain ɗin shi? Kai nasan ma ba shi da shi, kawai hala yana son Aisha ne yasa yake ga kaman mu ɗaya saboda nima suna na Humaira duk Aisha ne, to koma meye ne ohoo, ni dai bazan sake yadda ya mun maganan ta ba, kada wata rana naje ya mare ni, na faɗa ina zunɓura baki na gaba.

Har na kwanta barci babu alamar dawowar shi, ban ji daɗi a raina ba amma haka na kwanta, banda firgici da faɗuwar gaba babu abinda yau na keji cikin bacci na, wanda ko kaɗan bai mun daɗi ba, har a kayi asuba a haka na ta shi nayi salla, bayan nayi azkhar nayi karatun ƙur’ani na koma na ɗan kishingiɗa a kan sallayar.

Da safe ina tashi nayi wanka amma duk yadda na so na daina damuwa da rashin dawowar Dr abin ya ƙi barin zuciya ta, haka naje na dama quaker oats na sha a dole ba don raina ya so ba.

Wuraren ƙarfe 10:00 kiran Amal ya shigo mun, a hankali na ɗauka na kai kunne na, da ƙyar baki na ya amsa mata da sallaman da tayi mun, tambaya na tayi akan da yaushe zamu je shooping ɗin? Cikin kasala nace mata ta bari muje next week domin yau da ciwon kai na ta shi da shi, tausaya mun tayi sannan tace mu bari sai next week ɗin.

Ranar monday da naje school na ji ana cewa Dr Hussain yayi tafiya ba zai samu daman zuwa mana lectures ba, gaba ɗaya sai naji na nemi nutsuwa na na rasa shi, haka aka yi ta mana lectures amma bana ganewa.

Gaba ɗaya school ɗin da ƙasar sun fitar mun a raina, kasan cewar har ranan friday babu Dr Hussain babu labarin shi, duk wanda ya ganni yaga rashin nutsuwa a tattare da ni, domin tsabar zuwa duba ko Dr ya dawo har sai da muka saba da Peter da ɗaya neighbor ɗin mu mai suna David, don kullum na je in duba shi sai mun haɗu da su, har muka fara zama muna hira da su, wataran David zai ce na fito da books ɗina ya ɗan nuna mun wani abu, don yafi zaman hiran, saboda shi David bai cika son surutu ba, don shima alama ya nuna mayen karatu ne, dukkan su suna master ne a school ɗin mu, don bayan sun gama first degree ɗin su basu tafi ba, karatun su suka ci gaba da yi.

A haka kullum yamma za ka gan mu mu dukan mu ukun a zaune a ɗan wani wuri da aka saka kujerun ƙarfe, kuma wurin akwai shuke-shuke a wajen, don dama a wurin nake yawan ganin David yana karatu.

Har ranan friday ban ji ɗuriyar Dr Hussain ba, kawai sai na samu kaina da kwanciya kaman mai rashin lafiya, don ranan saturday ko fita kasa yi nayi, har a kayi sallar la’asar saiga Amal ta zo a kan muje shooping, babu yadda na iya dole na ta shi na shirya domin muje.

Ina shirin rufe gidan sai ga kiran Daddy ya shigo, jiki a saɓule na ɗauki wayan na kara a kunne na, ina jin kaman na saka mishi kuka.

“Sweet heart! Yaya na ji muryar ki wani iri, ko ba ki da lafiya ne?”.
Ya faɗa muryan shi cike da damuwa.

“Daddy kawai karatun yana yawa ne shi yasa nake jina kullum a gajjiye, yanzu ma har na kwanta na tuna a kwai shooping ɗin da za muje mu yi ni da Amal, shine na ta shi mu ka fito”.

“Sweet heart idan ba za ki iya zuwa ba ko zaki bari na gayawa Dr’n ku yazo ya kai ku? Don yanzu muka gama waya da shi yake ce mun shima yanzu haka yana hanyar dawowa gida, ina ga idan bai gaji ba ya kama ta yazo ya kai ku ko?”.

Ajiyar zuciya na sauƙe tare da runtse ido na, sannan a hankali na furta, “Daddy kuna waya da shi ne dama?”.

Dariyan Daddy naji sannan naji yana ce mun,

“Kullum sai mun yi waya da shi, kuma yana gaya mun irin ƙoƙarin da kike yi, yanzu ma haka yace mun kina kula da kan ki ba ki kula ƙawayen banza ko samarin banza, kuma naji daɗin hakan, don har nace shima yana tsawatar miki idan yaga za kiyi ba dai-dai ba, duk da nasan baki da problem ta nan Humaira na”.

Kallon inda Amal ta ke tsaye nayi, sannan na maida hankali na kan wayan ina tambayan Daddy,

“Daddy nan gidan kaji yace zai zo ko gidan wife ɗin shi?”.
Na faɗa ina tsoron kada Daddy yace mun can zai je.

Dariya Daddy yayi sannan yace mun,
“Gaskiya ni ban iya mita ba, don ban taɓa tambayan shi yaya matar shi ba, don shi ma bai taɓa gaya mun ba”.

Haka mu kayi sallama da Daddy, na ƙara sa wurin Amal mika wuce bakin titi domin zuwa shooping ɗin mu.

MAREMAGNUM MALL na gani rubuce a gaban mall ɗin da muka je, gaba ɗaya wurin sai naji ya tafi da hankali na, domin ba ƙaramin kyau ya mun ba, cikin jin daɗi da na ji damuwa na ya ƙaurace mun na wannan lokacin, muka saka ƙafan mu cikin mall ɗin.

Muna shiga Amal ta fara ɗiban abin amfanin ta, aka sari kayan maƙula she naga tana ta ɗiba, sai can kuma naga ta maida hankali wurin sayan cosmetics ɗin ta, Amal tana ɗan jan ƙafanta yau tunda muka fito, wanda alaman ciwon ta ne yake sanɗan ta, ganin kaman kayan ya fara mata nauyi, don sai ya mutsa fuskan ta ta keyi, ya saka na miƙa hannu ina mata murmushi na ɗauka mata.

ita ma murmushin tayi ta miƙa mun, sannan naga tayi hanyan wurin wasu takalma flats, ganin haka ni kuma nayi wajen turaru ka.

Dr Hussain? Dr Khadija economic lecturer ɗin mu ƴar india, su na gani a gaban turaruka suna zaɓan turare, gaba ɗaya Dr Khadija cikin fara’a take, ga wani azababben kyau da tayi da shigan su na sarii, wani Red colour da Golden a jiki, sai miƙo mishi su ta keyi tana nuna mishi, amma shi kuma fuskan shi a matuƙar ɗaure, kaman bai taɓa dariya ba, sai wani kakkaucewa ya keyi, gaba nane yayi mummunan faɗuwa, a zuciya ta nace.

Kaddai ita ce matar shi? Lokaci ɗaya na ji ido na ya ciko da hawaye, kuma ni ban ci gaba da abinda na keyi ba kuma ban tafi ba, ƙura musu ido nayi hawaye yana shirin zuba mun a ido na, ga wani zafi da bansan irin shi ba ya ziyar ci zuciya na.

Kaman ance ya ɗago kan shi, caraff Sai idon mu suka haɗu dana juna, dai-dai lokacin hawayen ido na suna gangarowa, wanda ko kaɗan ban san da zuwan su ba sai dai ɗumin su kawai naji, ƙura mun ido ya yi, yadda nima ƙura mishi ido na nayi.

Juyowa Dr Khadija ta yi don nuna mishi wani turaren da ta ɗauko, amma abin mamaki sai taga Dr ya ƙurawa wata ƴar ƙaramar yarinya ido, gaba ɗaya ji tayi ya ɗaure mata kai al’amuran, domin yaushe babbar mace ma ta ke ɗauke hankalin Dr ballanta na ƴar ƙaramar yarinyar nan, da ɓacin rai Dr Khadija ta juyo ta dubi Dr tace.

“Me ka ke nufi ne Dr?”.

Ko kallon inda Dr Khadija ta ke bai yi ba, kawai ƙura mun ido yayi shima yana kallo na.

Hararan shi nayi na juya na bi inda Amal ta ke, ita ma ta gama ta na nema na.

Wurin biyan kuɗi muka je na a jiye mata kayan, kallo na ta ke da mamaki amma bata ce mun uffan ba ganin yadda hawaye ke bin kunci na, haka aka buga mana aka bamu total, ɗauka mata kayan nayi har inda zamu hau taxi ba tare dana ce uffan ba, ita ma ba tace mun uffan ba.

Muna shiga sai gasu sun fito dukkan su ransu a ɓace, daga ganin su kasan a ɓace ran su ya ke, ƙura mishi ido nayi har muka bar wurin.

Muna isa gidan Amal naga ta ɗanyi jumm kaman baza ta fita ba, can kuma sai ta fita tana ya mutsa fuska, a hankali na dube ta nace, “Me yake faruwa da ke ne? Naga kaman ba kya jin daɗi ko”?.

Kallo na ta yi wanda idon ta gaba ɗaya sun ɗanyi kaman green kaman yellow, tana duba na fuska a ɗan ya mutse sannan tace,

“sister tun da yau na ta shi ƙafa na ya ke mun ciwo, amma na sha magani, idan Allah ya yarda zai yi sauƙi”.
ta faɗa ta na fita cikin dauriya.

Duban ta nayi nace, “sister ko dai mu tafi gida nane ki kwana? Kada na tafi ciwon ki ya tashi cikin dare, hankali na ba zai taɓa kwanciya ba idan na tafi na bar ki”.

Amsa mun tayi da “to”, sannan muka sallami taxi ɗin, kayan na ɗauka mata har cikin gidan ta, wanda suke su biyu ne a compound ɗin, har parlor na a jiye mata kayan, sannan ta ƙira Abban ta ta faɗa mishi yadda muka yi.

Karɓan wayan yayi ya mun godiya sosai, sannan muka ɗibi kayan ta da maganin ta, abin tausayi kafin mu fita a gidan sai da ts shafa wani magani mai ɗan karen zafi a ƙafan ta, wanda zafin sai dana ji shi har ido na, amma ita alaman bata ma jin zafin, haka muka fito muka tari taxi har gidan mu.

FATIE YAWALE, WANNAN SHAFI NAKI NE KYAUTA NA BAKI SABODA KASAN CEWAR KI ƘAWAS MAI BABBAN DARAJA A WURINA, ALLAH YA BAKI ƳAN UKU SAU UKU NAKE MIKI FATA, MASOYAN ANNABI SUCE AMEEN

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here