Home Daga Marubutanmu ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 29

ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 29

9
0

NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NICE✍🏼
@wattpad AuntyNice.

SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI

MISS XERKS (BESTY NAH)
AISHA ALIYU GARKUWA
UMMI GARKUWA (ZAIBAI)
SADNAF
NABILA RABI’U ZANGO
MAIDAMBU
KHALISAT HYDAR
wannan shafin nakune domin kuɗin daban ne a cikin duniyan marubuta, kunmun alkhairin da baki bazai iya furta kalman godiya ba, hannu bazai iya rubutawa ba, har abada godiyata da girmama AL’AMARIN ku bazan gajiya ba, NAGODE! NAGODE!! NAGODE!!! Allah ya kare mun ku da zuri’an ku duniya da lahira

SHAFI NA 29📑

__📖 Da sauri Faisal ya sakeni yana duba na a razane, domin shima ba ƙaramin razana yayi ba da jin irin ihun dana yi, ƙura mun ido yayi shi kanshi jikin shi rawa yakeyi, dai-dai nan mukaji buga ƙofa da ƙarfi.

A razane ya juya yana kallon ƙofan, domin jin muryan Ummi da Abbu, ta ɗayan gefen kuma Amaal ce ke ta faɗin, “sis Hummy ki buɗe ƙofan, mai ya sameki ne”? Da ƙarfinta ta ke ƙirana, ni kuma ganin hankalin mugun yayi jikin ƙofan, sai nayi wuff na faɗa toilet na danna key a jikin ƙofan, bansan lokacin da na furta “wayyo Dr nah, wayyo Daddy nah kuzo kada ya cuceni don Allah, kuzo ku fitar dani a cikin gidan”, da ƙarfina nake faɗi ina wani irin kuka kaman raina zai fita, don idan kun gani alokacin sai kunyi tunanin ko mutuwa aka mun.

Amaal ko da taji kuka na, gaba ɗaya jikinta ya ɗauki rawa tana duban iyayenta tace,”Ummi kuyi wani abu mana, bros ne hala a ciki, Ummi kada ya cutar da ita fah”, ta faɗa tana zubar da hawaye.

Jin haka ya saka Ummi ɗaga murya da ƙarfi tana ƙiran sunan Faisal, “Faisal ka buɗe ƙofan nan kuma kabar yarinyar nan, wallahi ka yadda wani abu ya sameta ban yafe maka nono na da kasha ba, ban yafe maka ba Faisal” ta ƙarisa faɗin kalmarta tana kifa kanta jikin Abbu tana kuka, cikin ɓacin rai Abbu ya sake buga ƙofan da ƙarfi yace, “idan baka buɗe ba Faisal yanzu zan ƙira securities su buɗe ƙofan kuma a tafi da kai a matsayin mai laifin raping, kuma kasan irin hukuncin da ƙasan nan zata yanke maka, secondly kuma zan yafe ka cikin ƴaƴa na.

Daga jin abin da Abbu ya faɗi Faisal da sauri yazo ya buɗe ƙofan jikin shi yana rawa, da sauri Ummi ta saka hannu ta wanke shi da kyakkyawan marin da sai dayayi namijin gaske kafin ya iya tsayawa da ƙafan shi, bai samu azaban ya sake shiba yaji sauƙan wasu tagwayen mari a fuskar shi, wanda da ƙyar ya samu nutsuwan gane daga inda suka fito, basu ankara ba kuma suka ga jini ya fara biyo hancin shi, saboda tsananin azaban mari, da ƙyar ya ɗaga kanshi ya dubi Abbu da yake wani irin hakki kaman zuciyar shi zai faɗo, da ƙarfi ya furta, “me kayiwa ƴar mutane Faisal? Na rantse da Allah idan ka cutar da ita zanyi shari’a da kai kuma zaka nisanta dani har abadan, shin kasan yarinyar Amana ce kuwa a hannun mu? Kasan yadda Mahaifinta yake jaddada mun riƙon amanan ta? Kaico da hali irin naka Faisal”, Abbu ya faɗa yana ƙara wanke shi da mari.

Muryan Dr sukaji daga bayan su yana tambayan, “Don Allah ina Aisha Humairan? Fatan dai bai mata komai ba”? Ya faɗa duk illahirin jikin shi yana rawa, suma cikin mamaki suke kallon shi, don basu san da shigowan shi ba, domin yayi sallama ya shigo suna gaisawa suka jiyo ihun Hummy, kuma sun manta da shi a wurin suka taho sama.

Amaal ce jikin ƙofan toilet ɗin tana ta bugawa tana ƙiran sunan hummy akan ta buɗe mata, ganin haka yasa Dr shigowa har inda Amaal ta ke ya jinguno da ƙofan muryan shi kaman zaiyi kuka yace, “Baby nah! Baby na ki buɗe mun ƙofan kada na shiga wani hali, ki buɗe na tabbatar da babu abinda ya sameki kafin numfashina ya ƙaurace mun”, ya faɗa duk dauriyar sa sai da hawaye ya zubu mishi.

Buɗe ƙofan nayi jikina yana kan rawa har lokacin, ga hawaye na kaman zasu ƙare a wannan ranan, ina kallon su bansan lokacin dana faɗa ƙirjin Dr na ba na sake wani irin kukan da bansan daga inda yaxo ba, muryata na rawa nace, “Dr na tsoron shi nakeji, nikan kamayar dani wurin Daddy na, tsoro nakeji Dr na”.

Da sauri ya kankame ni a ƙirjin shi, jikinshi yana rawa yake cewa, “Baby bai miki komai ba ko? Baby nah bazai miki komai ba insha Allah, kiyi shiru zan tafi da ke”, ina ƙara kankame shi ina kuma ƙara sautin kuka na nace, “Baby ya razana ni, ya bani tsoro, tsoron shi nakeji, ka gudu da ni, baby ina sonka kai ɗaya bana so ya mun wani abu ka tafi dani baby nah, na yadda kai kaɗai kake sona baka da niyyan cutar da ni”.

Kuka Amaal ta keyi kaman zata shiɗe, da sauri Ummi ta ƙaraso ta riƙeta tana faɗin kiyi shiru Amaal insha Allahu wani abu bazai taɓa faruwa da Hummyn ki ba mara kyau, kiyi shiru kada ciwonki ya tashi, da sauri na ɗago kaina daga ƙirjin baby nah, na ƙurawa Ummi ido, ganin ta juyo tana kallo na nayi sauri na tafi jikinta na rungumeta ina kuka, muryah a hankali tace, “babu komai doughter babu abinda zai faru dake insha Allahu, ki kwantar da hankalin ki kibar kuka, fatan dai bai miki komai ba”? Ta faɗa tana ɗago ni daga jikinta, ɗaga mata kaina nayi alaman ehh, sannan ta dubeni tace Amaal ta jirani mu shiryah sai mu same su a parloon ƙasa.

Dr yana bina da kallo da ƙyar yabi bayan su Ummi suka sauƙa ƙasa, ni kuma Amaal tazo ta rungume ni tana kuka, dukkan mu kukan muka saka muna rungume da juna, da ƙyar ta lallaɓa ni muka je na wanke idona, duk yadda tayi dani na shafa mai kasawa nayi, kawai wani dogon rigan atamfah na batik ta ɗauko mun acikin kayana na saka, da ƙyar na yadda ta shafa mun wasu turaruka a jikina, na ɗauki wani ƙaramin gyale green mahaɗin rigan na yafa shi akaina.

A parlor muna zuwa naga Faisal zaune a ƙasa wurin ƙafan Abbu, ɗayan gefen kuma Dr nane a zaune ya sunkuyar da kanshi ƙasa, Ummi kuma tana gefe kusa da Abbu suna zaune wuri ɗaya, shigowan mune ya saka dukkansu suka ɗago da kansu suna kallon mu, tsayawa nayi na kasa cigaba da tafiyan domin ganin Faisal zaune a wurin.

Ummi ce ta miƙo mun hannu alaman nazo wurinta, amma ganin Faisal kusa da su yasakani kallonta ban ƙarasa ba, idona na juya gefen da Dr yake zaune naga shima ido ya ƙura mun, kawai bansan yyh akayi ba kawai sai na samu kaina da tafiya inda yake, na zauna kusa da shi na takura sosai a jikin shi, kaman wani zaizo ya taɓa ni nake ji, lokaci ɗaya naji Dr yayi ajiyan zuciya, sannan ya saka hannunshi ya riƙe ni gam ajikin shi, shima a lokacin idan ka dube shi sai kaji kaman kayi kuka, domin gaba ɗaya a wani firgice yake.

Amaal ce ganin haka ta juya ta harari Faisal, murya a raunane tace, “Ummi Hummy na tsoron shi ta ke ji , kice ya bar wurin bazata iya zuwa wurinki ba”, ta faɗa tana share hawayenta.

Ummi ta miƙa mata hannu alaman tazo, haka Amaal ta ƙarasa ta kwanta gaba ɗaya a jikin Ummi, shi kuma Abbu yayi murmushi ya dubi Amaal yace, “ki barta a wurin Dr ta, yau inaga idan ba Daddyn ta ba toh babu inda zata samu nutsuwa idan ba wurin Dr ba, a razane ta ke sosai” ya faɗa yana dawo da kallon shi kanmu, nidai ban iya yin komai ba sai na ƙara matsawa jikin Baby sosai, har ina jin yadda jikin shi yake ta rawa, da sauri na ɗago kaina na dube shi, ganin ya ƙurawa Faisal ido kuma jikin shi sai rawa yakeyi, sai naji ya bani tausayi, a hankali na furta, “baby nah kayi haƙuri”, muryana ya fita a hankali kuma yana rawa, dawo da duban shi yayi kaina, sai naga hawaye suna zuba a idon shi babu kakkautawa, bakinshi har rawa yakeyi yace, “baby tsoro nakeji a cikin zuciyata, bana so tarihi ya sake maimaita kanshi akaina, ina tsoro sosai baby”, sannan ya juya ya dubi Abbu jikin shi yana rawa yace, “Abbu ka ƙira Daddynta kace yazo yau ya ɗaura mana aure, wallahi idan wani abu ya faru da Humairah bazan taɓa yafewa kowa ba, wallahi wannan karon zan ɗauki doka a hannuna, ina sonta sosai bazan iya barinta wa kowa ba, meyasa kullum saini? Me yasa kullum sai abinda nafi so? Wayyo Mama na! Wayyo Babana”, ya faɗa yana sauƙowa ƙasa inda nake zaune ya saka dukkan hannayen shi ya rungume ne dasu, kanshi ya ɗaura akan wuyana, muryan shi na rawa yace, “Baby kinsan ina sonki, idan wani ya sameki mutuwa zanyi, kinsan me yafaru dani abaya? Kinsan me ya baroni da family nah? Kinsan zafin danaji na rabuwa dasu? Kinsan gararin da rayuwata ta shiga ta dalilin wancan mummunan ƙaddaran? Toh yanzu kam mutuwa zanyi wani ya yi gangancin cutar mun dake, don ban taɓa jin irin son da nake miki ba akan kowa”, a hankali ya sake ni ya matsa a kusa dani ya ɗaga hannayen sama hawaye suna zuba a cikin idon shi yace, “Astagfirullah! Astagfirullah!! Astagfirullah!!! Allah na tuba, Allah don girman zatinka, don tsarkakayen sunayenka guda chasa’in da tara, don darajan wanda ka fifita fiye da kowa da komai, babban masoyinka annabin rahma, kayi mun maganin abinda ke faruwa dani da abinda yake faruwa da rayuwata, kaine masanin sirrin sarari dana ɓoye, nasan kafini sanin halin da nake ciki, da abinda ke faruwa dani,, Allah ka dubani da idon rahma kaji ƙaina ka sassauta mun abinda ke damuna, Allah kaine mabuwayi babu abin bautawa da gaskiya sai kai, a gareka na dogara, kaine mai kawar da baƙin ciki, mai yaye ɓacin rai, mai amsan addu’ar mabuƙata, Allah ka tsare mana gaban mu da bayan mu, Allah ka kare mu da aikata zina da luwaɗi da maɗigo, damu da ƴaƴa yenmu da na ƴan uwanmu, ka nisan tamu da aikata shi, Allah ka kare mun wannan baiwa taka, ka tsare mun ita daga dukkan sharrin masharrata, Allah ka kawo mun nutsuwa a zuciyata, Allah ka kare dukkan musulmai gaba ki ɗaya”, yana gamawa ya sunkuyar da kanshi ƙasa hawaye yana bin fuskan shi.

Hawaye Ummi ta share, tana duban mu cike da tausayi tace, “Abbu inaga ya kamata ka ƙira Daddyn tan, don bansan yayah Dr yakeji ba a ranshi, amma a matsayina na uwa nasan da ciwo a rayuwar shi, yakamata a hanzarta mallaka mishi Hummy”, ta faɗa tana ƙara rungume Amaal da take ta zubda hawaye.

Hmmm abin tausayi hattah Faisal kuka yakeyi, yana duban Dr yace, “don Allah Dr ka yafe mun, wallahi sharrin sheɗan ne, ni wallahi ban taɓa zina ba, kuma ban taɓa kusan tan shi ba, kawai sheɗanne yau yaso ya buga mun gangan shi, kuma Allah ya kare ni, wallahi dama a razane nake, na gode Allah kuma da kukazo, domin ni kuka taimaka, kuma nayi alƙawari ba Humairah ba ni ko waccce mace ma a duniya zan kiyaye kaina daga gareta, domin gudun faɗawa mummunan ƙaddara”, sannan ya riƙo hannun Abbu yana kuka yace.

“Abbu don Allah ku yafe mun wallahi nayi nadama tsakanina da Allah, kuma bazan taɓa maimaita hakan ba, kuyi haƙuri naci amanar tarbiyar dakuka daɗe kuna mun, wallahi wani abokina ne nagaya mishi yadda ake ciki, shi ne yace idan nayi raping ɗinta dole za a haƙura abarni na aureta, amma wallahi nayi nadama bazan sake aikatawa ba”.

Yana kuka ya ƙara sa gaban Ummi, riƙo hannunta yayi zaiyi magana amma sai ya kasa, domin ganin irin kukan da Ummi da Amaal sukeyi, kawai sai ya rungume su duka yana faɗin, “Ummi nah, Ummi nah ki daina mun kuka kada Allah yayi fushi dani, na tuba Ummi na”, ɗagowa Ummi tayi tana shafa kanshi tace, “na yafe maka Faisal kuma nayi imani da Allah ba halinka bane na yadda sharrin shaiɗanun abokaine yake wasa da rayuwar ka, kuma na raba ka da wannan abokin, na kuma raba ka da hidiman mace idan ba ka tashi aure bane, ni ina kuka domin tausayawa Dr ne, amma bana zubar maka hawaye, domin ina addu’an Allah yasa ku gama damu lafiya, ku gama da duniya lafiya”.

Gyaran murya Abbu yayi, kowan mu sai da ya ɗaga ido ya ƙura mishi, jiki a sanyaye Abbu ya saka tissue ya sha re hawayen dayake ta biyo kan kyakkyawan fuskar shi, a hankali ya dube mu gaba ɗayan mu, sannan ya sauƙe idon shi akan Faisal yace, “Ɗana Allah ya kare mun ku daga sharrin abokai da rayuwa, kuma ni bazan ce na yafe maka ba har sai naga hummy ta bar gidan nan lafiya, kuma ina mai ƙara jan hankalinku daku ji tsoron Allah a duk inda kuke, kuma kada kayi tunanin cewa aboki ya sakaka a abu, toh wallahi ranan lahira Allah zai maka hukunci da abinda ka aikata, bawai za ace a barka ba saboda kai abokine ya saka ka, shiyasa ake so ayi abota dana gari, kuma wallahi duk inda kake kasa ka tsoron Allah a zuciyar ka, babu abinda yake cikin zina sai masifa da azaba, kuma sai anrama kaima akanka watarana”, sannan Abbu ya dubi Ummi yace, “Muma muna da laifi domin mun bar Faisal yana shiga ɓangaren Amaal kaman ɓangaren namiji ɗan’uwan shi, kuma hakan babban kuskure ne, shiyasa yanxu alfasha yayi yawa ko acikin ƴan’uwa ma, amma insha Allahi daga yau nayi duba da kuskuren mu, daga yau Faisal ka tsaya iyaka naka ɓangaren sai kuma nan parlor, amma bana so ka ƙara zuwa ɗakin Amaal, kema Amaal ban yadda kije ɓangaren shi ba daga yau, sai kuma mu nemi yafiya a wurin ubangiji”.

Dawo da kallon shi yayi kaina yace “Humairah kiyi haƙuri, bansan haka zai faru ba amma duk da haka kiyi haƙuri insha Allahu zamu ƙara saka ido akai”, sannan ya dubi Dr yace, “kai ma kayi haƙuro Dr da yadda aka ɗaga maka hankali, kuma insha Allahu zan ƙira Daddynta zan mishi bayani kuma inda hali zan ce mishi yazo nan ya same mu sai muyi dukkan magana da zamuyi a nan, ina fatan kowa zai yafewa ɗan uwanshi”, gaba ɗaya kowa ya yafe wa ɗan’uwan shi, sannan akace mu tashi mu tafi ɗaki, ɗago ido nayi ina kallon idon Dr, wanda shima kallo na yake, da ƙyar ya sake mun hannu na ya tashi ya yi sallama dasu Abbu ya tafi.

Jikina a sanyaye na riƙe hannun Amaal muka wuce ɗaki, inda muka bar Abbu da Ummi da Kuma Faisal a parlor.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here