NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NICE✍🏼
SHAFI NA 28📑
__📖 “Yayah zaka shigo har gidan iyayena kuma ka rungume matar da zan aura a gaban ido na? Kasan duk wani abinda na maka kai kajawo”.
Murmushi dr na ya sake yi yana duban Faisal da ya koma kaman wani ɗan ta’adda, sai wani zare ido yakeyi kaman tsohon maye, “saurayi kayi haƙuri nazo har ƙofan gidan mahaifinka ina ɓata maka rai, very sorry ƙanina ban so hakan ba, matsalan da aka samu na biyo wife ɗinane, amma babu komai zamu kiyaye”, Dr ya ƙarasa faɗa yana ta zuba smilling yana kallon idona.
Ban shiryah ba nima na samu kaina da maida mishi martanin murmushin, wanda gaba ɗaya muka maida Faisal kaman wani gunki a tsaye a kanmu, ranshi a matuƙar ɓace yaja tsaki ya wuce cikin gidan yana ta wasu ƙananun surutai wanda bamu jin abinda yake faɗi.
Dawo dani gaban shi Dr yayi yana duban cikin idona, cikin nuna mun zallan so da ƙauna yace, “Baby nah don Allah ki kula mun da kanki, kinsan dai yaran larabawa ba kirki bane da su akan mace, saboda haka don Allah ki maida hankali da yaron nan, don akwai rawan kai na yarinta a kanshi sosai”.
Murmushi nayi ina mai ƙara damƙe hannun shi nace, Dr nah baka da matsalah da wannan, insha Allahu zan kiyaye babu abinda zai faru da yardar Allah, nidai kawai bana son wulaƙanta shi ne bayan nazo gidan su”.
"Toh ce mishi akayi kema baku da gida? Yasan ae kin wuce sa'ar shi a maganan soyayyah amma banda rawan kai irin na yara zai wani tsaya cike da rashin kunya a gaba na ko? Toh ya maida hankalin shi kan karatu yabar masu abu da abinsu", ya faɗa yana kanne mun ido ɗaya, "baby kinga abunda nake gudu da sauƙa
a gidan nan ko? Yanzu yaron nan da anan na sauƙa zai dawo yana mun rashin kunya na kwana a gidan su ina mishi hira da mata, while kuma matar tawa ce”.
Murmushi nayi na sake hannun shi, marairecewa yayi shi ba zai tafi ya bar ni ba, da ƙyar na sha kanshi mukayi sallama na dawo ciki.
A parlor na same su suna zaune dukkan su, daga Abbu har Ummi suma suna zaune, gefe ɗaya kuma Amaal ce zaune a kusa da Ummi, chan kan dinning kuma rasa kunya ne yake cin abinci.
Zuwa nayi kusa da Amaal na zauna ina duba abinda ta keyi cikin wayanta, murmushi tayi ta ɗago mun screen ɗin wayan don naga abinda ta keyi, “abinda kika fita yi nima shi nakeyi daga nan magulmaciya”, ta faɗa ƙasa-ƙasa yadda ba mai jin mu tana dariya.
Nima dariyan nayi na sunkuyo dai-dai kunnen ta nace, “naku salon ba irin namu bane, mu bamu kwaikwayo amma ke gashi kinayi”.
Hararana tayi tace, “me na kwaikwaiya ƴar rainin wayo”?
Dariya nayi ina buge bayan ta nace, “dubi abinda yake kan screen ɗinki kiga yadda kika kwaikwaye mu nida Baby”.
“Toh mayun soyayyah an kwaikwaya ɗin, tashi ma a kusa dani ki dena ƙare mana tanadi”.
Ummi ce ta dube mu fuskan ta ɗauke da murmushi tace, “sirrin me kukeyi ne ƴanmata nah”?
Dariya nayi na ƙara sa gefen Ummi na zauna a ƙasa kusa da ƙafanta ina dariya nace, “Ummi kwaikwayon mu da Dr suke yi, yanzu naga ta tura mishi txt wai baby nah me kake yi? Bayan salon mu ta kwaikwaya”, na faɗa ina ɗaura kaina akan cinyan Ummi ina dariyan Amaal da ta buɗe baki tana kallona.
“Ashe Hummy har yanzu kina nan da halin ki na kwafsi? Toh wallahi idan kinyi wasa kema zan faɗi abinda kike turawa Dr”.
Abbu ne ya kalle mu yace, “yau kuma fallashe-fallashe akeyi a gidan nan ko?” sannan ya dubi Faisal da yake ta howa yace, “kaima kazo kaji tonan asiri da ƙannen ka suke yi, kaima kazo muji ko sun san naka”, Abbu ya ƙarasa da murmushi a fuskar shi.
Ya mutsa fuska Faisal yayi yana turo baki yace, “Abbu ae ni Humairah nake so, amma naga wani hali da sis Amaal ta ke nuna mun akan wani chan daban”, ya faɗa yana hararan Amaal, gefe na yazo ya zauna kusa da ɗayan ƙafan Ummi.
“Amma baka da hankali ne son? Yarinyar da ta ke da wanda ta ke so, yasan mu, mun san shi zaka ɓullo da wani shiririta kuma? Kai kan ae matar ka bata wuce ss1 ba a secondry, saboda haka kada na ƙara jin wannan shirmen a bakin ka daga yau”, Abbu ya faɗa cike da ɓacin rai.
“Gaya mishi dai Abbu don na lura Faisal yana son ya chan ja halayen shi masu kyau da muka san shi dasu zai kwaso wasu, kuma hakan ba dai-dai bane, da wani ido Dr zai kalle mu? Wanda basu san alƙawari da amana ba?
Faisal sai wani ƙara tamƙe fuska ya keyi yana hararan Amaal a fakaice, wanda ita kuma sai murmushin iya yi ta keyi, nidai kasa ɗaga ido nayi na dubi kowa, wasa kawai da yatsuna nake tayi, domin koma meye Faisal ya ban tausayi, domin ganin yadda kowa ya nuna mishi bai kyauta ba sai yaban tausayi.
“Humairah bana son ki bar yaron nan ya shiga rayuwar ki, domin bazan ji daɗi ba idan Dr ya fahimci da akwai shirmen Faisal na cewa yana sonki, zanji kunya don zai ganni ƙaramin mutum, na ɗauko ki na kawo gidana, ɗana kuma yana nemanki, gaskiya bazan so faruwar haka ba, kaima ka kiyaye kana jina ko Faisal”? Abbu ya faɗa cike da ɓacin rai.
Amsawa a hankali Faisal yayi cike da jin haushi, bai kuma ɗau wani lokaci ba ya tashi yayi sallama da kowa ya wuce ya bar parlon.
Ummi ce ta bishi da kallo fuskanta ɗauke da murmushi tace, “in banda rikici irin na Faisal ina zai kai Hummy? Kawai neman kada a zauna lafiya ne”, Abbu ya harari ƙofan da yabi yace, “shiririta dai irin na yara, amma ae Humairah ba sa’ar shi bace”.
Dariya Amaal ta kwashe da shi tana kallon Abbu tace, “Abbu sai kaga irin hararan da ya bini da shi, kuma ina ganin sai da ya ta ke hannun Hummy kafin ya bar wurin, amma ta yi wani shiru bata ce komai ba, da nine kan ae sai gadon asibiti”, ta ƙarisa faɗi tana dariya.
Kowa a parlon dariya ya fara Ummi tana duba na tace, “doug kodai kina son shine kada muyi shishshigi”? Dariya nayi na sunne kaina akan cinyan Ummi .
“Ta isa tace tana son wani bayan Dr”, inji Abbu. “ae sai na ɗaura auren gobe naga yadda zata saurari wani, shima Faisal rikici ne ae”.
Hutun mu tare da Dr yamana daɗi sosai, don kullum sai yazo ya fita damu, mune zuwa shan ice-cream, mune zuwa nan mall ɗin muyi shooping, wataran muje park mu zauna ayita shan soyayyah, gaba ɗaya rayuwar sai naji ban taɓa jin daɗi irin na wannan lokacin ba, a haka har hutun mu ya ƙare, a na saura 2dys mutafi, shi kuma Faisal ranan ya koma school, lokacin da zai tafi ya shigo har ɗakin Amaal, dai-dai lokacin na fito daga wanka ɗaure da towel a jikina.
Faisal yana shigowa ya tsaya ya ƙura mun ido, ganin kallon na shi bana ƙare bane jikina a ɗan firgice nace, “kana neman Amaal ne”?.
Ina jiran naji amsan da zai bani amma sai naga ya maida ƙofan ya rufe ya kuma murɗa key ɗin ɗakin.
Wani irin mummunan faɗuwar gaba naji ya zo mun, wanda har sai da naji kaman wani guntun fitsari ya ɗigo mun, jikina yana rawa na sake tambayan shi, “Amaal kake nema ne bros”?
Munafukin murmushi yayi yana matsowa inda nake tsaye yace, “wurinki nazo muyi sallaman da kowa bazai taɓa mancewa da ɗan’uwan shi ba har ƙarshen rayuwar shi, kuma ina so yau ki yadda dani kika dace ba wannan tsohon ba”.
Juyawa nayi da sauri zan koma cikin toilet ɗin, amma sai naji charaf ya chafke ni.
Ban san lokacin da na zunduma wani uban ihu ba iya ƙarfina.
Ni Aunty Nice nima sai da naji zuciyata zata buga domin jin irin ihun da Humairah tayi, wanda sai danaji shi har cikin ƙwaƙwalwata, wanda naji typing ɗin ma yana neman gagara na, don ni kaina na razana da Faisal, amma kada ku gajjiya da alƙalamin Aunty nice, ku jiraye ni zuwa bayan sallah idan Allah ya kaimu da rai da lafiya, kuma kada kumanta da naman sallah, kowa ta ƙullah mun na bawa Babyn Baby.




