Home Daga Marubutanmu Ƙaddara Ta Riga Fata: Fita Ta 17

Ƙaddara Ta Riga Fata: Fita Ta 17

3
0

NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NICE
@wattpad AuntyNice.

SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI

SHAFI NA 17

Muna cikin haɗa girkin Amal ta ƙira brother ta Faisal, suka shiga tsara yadda zasu dinga ɗaga hankalin Dr Hussain, nidai sai dariya da sha’awan su kawai nakeyi, domin a handsfree ta bar wayan, burgeni sukeyi kaman wasu friends.

Ina sauraren su ina ɗan dariya ƙasa kasa, chan naji muryan Faisal yana cewa, “ina ƴan mata na ɗin? Bani ita naji muryanta”, dukkan mu dariya mukayi tukun ta miƙo mun wayan na kara a kunne na.

“Hello sweety” ina dariya nima nace, “hello honey” dukkan mu dariya mukayi, sannan ya dinga tsara mun yadda zan dinga amsan wayan shi a gaban Dr, haka mukayi ta hira har muka gama girkin mu, ƙamshi kam nasan ba gidan Dr ba, yau inaga hatta gidan su Peter ma sai sunji.

8:30pm dukkan mu munyi wanka, dogon riga muka saka kowa ta yafa ɗan gyalen kayan, ɗiban abincin mukayi dukkan mu muka fita zuwa gidan Dr.

Bamu daɗe muna knocking ba yazo ya buɗe mana, har zuwa lokacin fuskar shi a ɗaure, haka ya bamu hanya muka kai abincin har kan dinning ɗinshi, wucewa yayi parlor ya chigaba da kallon shi batare da ya kalli inda muke ba, ganin haka Amal ta mun signa, dariya nayi na wuce inda yake na zauna a hannun kujeran ina leƙa fuskan shi ina murmushi.

“Babyn baby yau na maka girki mai daɗi, taso muje na zuba maka kaji daɗin shi,”? ……harara na yayi sannan ya juya ya kalli inda Amal ta ke zaune, ganin hankalinta yana kan wayanta sai ya dube ni yace, “bazan ci ba ni naƙoshi”.

“Haba babyn baby! Ko kafiso yau na kwana banci komai ba? Kuma na kwana ina kuka”? Na faɗa kaman zan fara mishi kukan a lokacin.

Sake duban inda Amal ta ke yayi, sannan yace, …..”baki damu da ni ba ae, toh me yasa zaki damu da cin abinci na”?

“Duk duniya babu wanda ya damu da kai bayan ni, kuma na damu naga kaci ka ƙoshi, saboda nafi so na dinga ganin ka cikin kwanciyar hankali”, na faɗa ina tashi tsaye domin mu wuce dinning ɗin.

Tashi yayi ya tsayah yana kallona ido cikin ido yace, “waye darling forever”?

Juya ido na nayi sannan na lumshe su na buɗe, “nafi damuwa da naga kachi ka ƙoshi sama da maganan darling forever, saboda haka muje na samu nutsuwanka tukun kafin wani yabiyo baya”.

Amal ta riga mu gama cin abinchin, sai ta kamo cikin parlon ta zauna jiran mu, channels ɗin take ta chanjawa, muna gama ci na miƙe zan tafi, da sauri yace, ……”dawo ki bani labarin shi, kuma daga yau idan kungama girkin ki ƙirani a waya zanzo gidanku kawai muna ci achan, bazan so ku wahala kullum wurin ɗaukan kaya ba” ya faɗa yana sauƙe mun kyawawan idon shi akaina.

Bansan meyasa nake yawan jin kunyar shi ba idan ya kalle ni, murmushi nayi na sunkuyar da kaina ina kallon yatsuna ina wasa da su.

“Faisal matashin yaro ne fari kyakkyawa mai nutsuwa da ilimi, faisal farin balarabe ne ɗan gata a wurin Ummi da Abbu, Faisal shine ɗa na farko a wurin iyayen shi, yana karatun medicine a oxford university, yana shekaran shi ta ƙarshe, Dr nah ina matuƙar ƙaunar Faisal, saboda irin so da kulawan da yake nuna mun, faisal ba ya haɗa soyayyata da ko wacce mace a duniya, kodan babu wanda ya taɓa sonane sama da nashi? Oho inaga don duk duniya babu mai mun irin soyayyan shi shiyasa nake ganin hakan”….”ƙarya ya keyi bashi kaɗai bane yake sonki, ƙarya ne shiɗin ba sonki ya keyi ba yaudara ne, ina ma yasan kanshi ballanta na ya soki”!? Cikin tsawa yake maganan bayan ya miƙe ya tsaya a kaina.

“Kada ki sake barin zuciyar ki ta yarda wani yana miki so sama”…….
sai kuma yayi shiru yana kallon Amal da ta taso ta miƙo mun waya tana “ga bros yana ƙira”, tana miƙa mun ta ɗauki kwanokan tayi hanyar fita a parlon, ni kuma ɗauka nayi fuskana cike da murmushi, amma ƙasan zuciyata kaman na ranta da gudu,

“Hello honey nah”! Banji amsan da Faisal ya bani ba kawai naga wayata a hannun Dr, kashe wayan yayi sannan ya nuna ni da yatsan shi.

“Duk abinda ya ke rawa a kanki Aishatu zan ɗaure miki shi, baki da hankaline a gabana zaki tsaya kina waya har kina ƙiran wani ƙaton banza wai Honey? Bakida tunani ne? Toh daga yau ki bashi haƙuri kigaya mishi gaskiya karatu zakiyi ba soyayyah ba, nawa ma kike da zaki damu kanki da soyayyah”?

Juyi na farayi a gabanshi ina magana cikin shagwaɓa, ” Dr mu dubi fa wallahi na girma, kuma ni sonshi ya mun yawa kaman bazan iya karatun ba ma gara a mana aure kawai”, na faɗa ina ɗaura hannu na a gefen heart ɗina ina wani lanƙwashewa kaman tarwaɗa.

ya daɗe yana kallona, sannan murya a hankali ya nuna mun hanyar waje yace,
“fita don Allah kije ki ƙarashi fitinki wa Amaal, amma nikan nawa ya isa haka, wuce kifita”, ya faɗa kaman idan ya buɗe baki yayi magana da ƙarfi zuciyar shi zata faɗo.

Buga ƙafa na fara a wurin ina nikan bazan tafi ba sai kabani wayana, kasan fah zai ƙirani anjima, kuma ni sai ka rakani Dr nah”, na faɗa ina kan dire ƙafan a ƙasa.

Riƙo hannuna yayi muka nemi wuri muka zauna, yana duba na a nutse yace, “Don Allah ki taimake ni ki rabu da yaron nan, bana so naga kina son kowa Humairah, ban shiryah samun damuwa ba a tsakanin mu yanzu, don Allah ki barshi bana so, ko baki so na samu kwanciyar hankali ne”?

“ina so mana Dr mu”.”tunda kina so toh bana so naga kina son kowa idan kin tashi aure ni zan zaɓa miki miji, amma yanzu karatu na fi so kiyi kinji baby nah!”

Turo bakina nayi gaba ina kallon shi kaman zanyi kuka nace, “Dr nifah auren shi zanyi, ina son shi fa sosai, da ƙyar fa nake iya bacci this days, daga na kwanta sai na fara mafarkin munyi aure ya kaini mall, wataran har yara ma na ke ganin mun haifa kaman yaran Larabawa”.

“Ya rabbi! Don Allah ki daina kwantan ta kanki da wani namiji baby, har kina tuna wai zaku haihu tare? Zaki kashe ni ne kawai kwanana bai ƙare ba”, ya faɗa yana matse yatsun hannu na da ƙarfi, wanda har saida nayi kara da ƙarfi tukun ya sa ke su.

“Baby kaima fah kana da mata, toh ni me zaisa bazanyi aure ba”? “ni banida wata mata” ya faɗa da ɗan karfi yana ƙura mun ido, nima ƙura mishi idon nayi cike da mamaki, bakina a buɗe nace, “Dr Khadijah fah”?

“Ni ba mata ta bace, ita take shirmenta, ke kuma kika dame ni wai mata ta ce, ni tunda nazo ƙasan nan ban taɓa son kowa ba sai mace ɗaya, ni kuma ban taɓa aure ba har yanzu”.

Gaba na yana faɗuwa ina duban shi nace, “wacece ka taɓa so a ƙasan nan? Toh meyasa na ganka da Dr Khadijah ranan a wuri ɗaya? Idan ba sonta kake yi ba mai ya haɗa ka da ita”? Na faɗa kaman wata mai tohuman ɗan ta.

Sake riƙo hannuna yayi cikin ƙasa da murya yace, “nidai bana son Khadijah, kuma ban taɓa sonta ba ballantana na aure ta, amma na miki alƙawari idan kin rabo da yaron nan zan baki labarin komai game da Khadijah”.

“har wanda ka taɓa so zaka bani labarinta”? Yana murmushi yana duban ido na yace, “har su Hassan ɗina, Ummi nah da Abba na duk zan baki labarin su, amma sai kin mun alƙawari bazaki sake kula kowani namiji ba, kuma ba zaki so ko wani namiji ba sai wanda na zaɓa miki”.

Shiru nayi na zuba mishi ido, ganin yadda shima ya ƙura mun ido, “toh nima kamun alƙawarin bazaka so ko wacce mace ba, idan ka so wata nima zan so faisal, don yana da kyau kuma fari ne”.

“Baby ya kai ni kyau”?

Kallon Dr nayi bakina a buɗe nace, “nifah ban taɓa ganin mai irin kyaunka ba, kaifa kyaunka mai kyau ne”.

Runtse ido yayi zuwa chan ya buɗe su a kaina, “tashi muje na rakaki dare yayi, kuma Amal zata gajji da jiranki”, ya faɗa bayan duk mun tashi mun tsaya muna kallon juna.

“Baby kina da”…. Sai kuma yayi shiru yana murmushin da yake cije leɓen shi, turo baki nayi nace, “baka ƙarasa ba”.

Dariya yayi ya jawoni mukayi hanyan waje, a waje mukaga David da Peter suna shigowa gidan, zuwa sukayi suka gaida Dr, sannan Peter ya dubeni yace, “preety yau kinyi kyau sosai, kaman wata star”, ya faɗa suna wuce gidan su suna dariya.

Nima dariyan nayi na matso kusa da Dr nace, “kai kaɗai ne baka taɓa ce mun ina da kyau ba, kowa sai yace kyauna yayi yawa ma, amma kai ko kaɗan baka taɓa cewa ba”, na faɗa ina hararan shi.

Yana rako ni ya tsaya yana mun wani duban da har saida naji tsikar jikina yana tashi yace, “bana son kibar su Peter suna cewa kina musu kyau, bana jin daɗi, sufa students ɗinane, bana jin daɗi gara ki hana su”.

“zan gaya musu su daina, amma da gaske goben komai zaka gaya mun”?

“idan kin daina son Faisal ba”, ya faɗa yana komawa gidanshi, bayan ya sake mun hannu na.

Ina shiga Amal ta taso tana tambayana yadda akayi? Labarin abinda ya faro na mata, haka mukayita dariyan shi, duk da Amal ta mun masifan me yasa nace yana da kyau, meyasa kuma nace, shi bai ganin kyau na?.

Hararanta nayi nace, “ce miki akayi ina sani ne nake gaya mishi? Kawai idan ina tare da shi manta kowane shawara kuka bani nakeyi, sai ɗaɗɗaya, kedai Allah ya kaimu goben muji labarin komai.

NIMA AUNTY NICE NACE ALLAH YA KAIMU GOBEN DA RAI DA LPY, IDAN KUNA BIYE DA ALƘALAMINA ZAMUJI ME ZAI KASANCE A TAAKANIN SU

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here