Home Labarai ‘Yan sanda sun kama wani saboda walaƙanta Alƙur’ani a Kebbi

‘Yan sanda sun kama wani saboda walaƙanta Alƙur’ani a Kebbi

29
0

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi ta kama wani Abubakar Musa Mai shekaru 29 a ƙauyen Rafin Mose a ƙaramar hukumar Zuru jihar Kebbi kan zargin haɗa baki a aikata manyan laifukan walaƙanta Ƙur’ani da kawo hargitsi a cikin jama’a da  neman mallakar mace ba da sonta ba da sauran laifukan.

Hukuma ta soma bincike kan zargin mijin Zara’u Hassan waton  Rabi’u Tela da wasu mutane biyu da suka binne kwafin Alƙur’ani, maniyyi, goro fari da ja, kayan ciki na  mutum na sawa(tufafi), matattun dabbobi da wasu abubuwan surkulle a cikin rami da aka haƙa a ɗakin matarsa, Zara’u, a unguwar Zango kwana huɗu da suka wuce .

 Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, SP Bashir Usman, ya fitar da bayani a ranar Jumu’a cewa rundunar ta kama wani Abubakar Musa, mai shekaru 29, mazaunin Rafin Mose a Ƙaramar Hukumar Zuru, bisa zargin haɗa baki da Rabi’u Tela da Hamza Zango wajen haƙa rami a ɗakin matarsa  da binne abubuwan da aka ambata domin ya mallake ta sai yanda ya so da ita.

Sanarwar ta ce, Rabi’u Tela da Hamza Zango sun tsere kuma rundunar tana ci gaba da ƙoƙarin kamo su.

Binciken farko da rundunar ta gudanar ya nuna cewa ana zargin an aikata wannan abu ne da nufin sanya Zarau Hassan ta fi biyayya ga mijinta Rabi’u Tela, lamarin da rundunar ta ce yana da yanayin da ka iya haddasa tashin hankali tsakanin Musulman yankin.

Sanarwar ta ce, abubuwan da aka binne sun haɗa da kwafin Alƙur’ani, maniyyi, goro fari da ja, kayan ciki da mutum ke sanyawa, matattun dabbobi da wasu abubuwan surkulle da rundunar ta bayyana a matsayin na tsafi. 

Ta ce Abubakar Musa wanda shi ne Bokan yana tsare hannunsu za su kai shi kotu da sun kammala bincike.

Kwamishinan ‘yan sanda CP Umar Haɗeja ya yi tir da faruwar lamarin ya yi gargaɗi domin ba za su yi wasa da lamarin ba, za a ɗauki mataki ga duk wanda yake walaƙanta addini da kawo cikas ga zaman lafiyar mutane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here