Home Politics Zaɓen Osun Gwamna Adeleke na kan gaba da ƙuri’u 177,572

Zaɓen Osun Gwamna Adeleke na kan gaba da ƙuri’u 177,572

29
0

Adeleke na jam’iyyar Accord na kan gaba a zaɓen gwamnan jihar Osun da Kuri’u 177,572

Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya fara samun rinjaye a yayin tattara sakamakon zaben gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar.

Jaridar Punch ta rawaito cewa, bayan tattara sakamakon rumfunan zabe 303 daga cikin mazabu 332 na jihar, Adeleke na jam’iyyar Accord ya samu kuri’u 177,572, kwatankwacin kashi 50.5 cikin 100.

Dan takarar jam’iyyar APC, Bola Oyebamiji, ne ke biye da shi da kuri’u 158,588, wanda ya yi daidai da kashi 45.1 cikin 100.

A matsayi na uku kuwa, Najeem Salaam na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ya samu kuri’u 5,917.

Rahotannin tattara sakamakon sun nuna cewa daga cikin masu rajistar zabe 845,100 a jihar, an tantance masu kada kuri’a 361,500, wanda ke nuna yawan fitowar masu kada kuri’a da kashi 42.8 cikin 100.

An samu kuri’u masu inganci 351,500, yayin da aka soke kuri’u 7,200.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa zuwa lokacin da tattara sakamakon ya shiga matakin karshe, kashi 43.41 cikin 100 na rumfunan zabe ne suka mika sakamakonsu.

Adeleke, wanda ke neman wa’adi na biyu, ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa Accord kafin zaben. INEC ta amince da jam’iyyu 14 su fafata a zaben bayan PDP da Labour Party sun kasa gabatar da ‘yan takara.

Ana sa ran INEC za ta bayyana sakamakon karshe tare da sanar da wanda ya lashe zaben ta hannun jami’in tattara sakamakon jihar, bayan kammala karbar dukkan sakamakon mazabu da suka rage.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here