Home Manyan Labaru ‘Yan sanda sum fatsama don  kuvutar da mutane 39 da’yan bindiga suka...

‘Yan sanda sum fatsama don  kuvutar da mutane 39 da’yan bindiga suka tsare a lokacin da suka je zaman sulhu a  Zamfara

13
0

Runduna ‘yan sandan jihar Zamfara ta fara yunqurin kuvutar da mutane 39 da ake zagin ‘yan bindiga dake yankin Magamin Diddi a qaramar hukumar Maradun sun yi garkuwa da su bayan da suka tafi zaman sulhu da su.

A cewar ‘yan sanda rahoto ya zo masu daga ofishinsu na Maradun in da mai garin Magamim Diddi ya zo masu da labarin kama mutanen a ranar Lahadi.

  A rahoton mutanen su 47 sun haxa kansu suka shiga dajin Fadama domin yin zama da uwayen hatsabibin jagoan ‘yan bindiga waton  Jimo smally a manufarsu ta samun sulhun zaman lafiya a tsakaninsu.

A lokacin da zaman ke gudana sai xan bindiga da yaransa suka zo wurin suka yi garkuwa da mutum 39 suka tafi da su wani wuri da har yanzu ba a sani ba.

Bayan da ‘yan sandan Zamfara  suka samu labarin sun gaggauta xaukar matakin baza komarsu don ganin an gano in da mutanen suke da kuma kuvutar da su, yanzu haka jami’an tsaro suna aiki da bayanan sirri domin ganin an kuvutar da mutanen.  

A bayanin da jami’in hulxa da jama’a na rundunar DSP Yazid Abubakar ya fitar ya ce rundunarsu ta tabbatar za ta kuvutar da mutanen ta kuma hukunta waxanda suka yi garkuwa da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here