Matsalar tsaro na kara ta’azarra a jihar Sakkwato da yawan wararen da ke da zaman lafiya a baya a yanzu suna fuskantar matsalar ‘yan ta’adda suna yi masu abububwan da kamar turo su aka yi wurinsu na tabbatar da hana masu zaman lafiya, a satin da ya gabata ‘yan bindigar suka shiga karamar hukumar Kebbe suka ta’asa wadda ba a taba yi ba a yankin, abin da ya kai ga mutanen garin yin Allah wadai ga Gwamnati tare da yin tambayar laifin mi suka yi da gwamnati ta saka idanu ana kashinsu yanda aka ga dama.
Ashiru Muhammad Sani Kebbe, ya ce rana jumu’ar data gabata mutane sun fita zuwa gonakinsu a wajen gari, kawai sai ga mutanen da suka tafi daji suka dawo da gudu suka ce ga barayi nan zuwa sun fi 500 kan babura kowanensu saman goyon mutum uku, da suka shigo garin ne sojojin da ke aikin samar da tsaro a yankin suka tunkare su, ana harbe-harbe da su, ashe wasu sun fito masu ta baya suka zagaye sojojin ta ko’ina, sojojin sun yi kokari matuka don suga barayin ba su shiga garin Kebbe ba amma sun fi karfinsu sai da suka kashe sojoji hudu dole suka gudu suka bari ‘yan bindigar suka shiga garin Kebbe suka shiga in da suke so suka yi abin da suka ga dama.
“Ana haka suka shiga kauyen Kaya suka kashe mutum uku, Barga da Unbutu suka yi satar dabbobi, Aungushi a can ne suka yi barna sosai suka kashe mutane 32 suka sace dabbobi ba adadi, sun kwashe kayan shaguna.”
“Wannan ne karo na farko da maharan suka shiga cikin garin Kebbe a haka da yawa, a baya sukan shigo a sace su dauki wani su fita ko su shiga kauyukkan garin, a yanzu Kebbe da makwabtanmu ba wanda yake cikin hayacinsa, a yanzu kauyen Gwandi da Ungushi sun zama kufai kowa ya watse an sace rakuma da shanu da Akuyoyi sun kone motocin mutane bayan kisan gilla da suka yi, a halin da ake ciki mutane sun watsu suna gudun hijira, wasu a garin Kebbe suke suna neman mafaka ba tare da an ba su wuri daga gwamnati.”
Ya koka kan sakacin hukumomi da gwamnati kan ta’azarrar lamarin, “a lokacin da suke garin Ungushi jirgi ya zo ya yi shawagi amma ba wani dan ta’adda da aka kashe, ni na yi Allah wadai da rikon sakainar kashi da gwamnatin tarayya da jihar Sakkwato suka yi wa sha’anin tsaro musamman namu, tun Juma’ar da aka kai mana hari har yanzu babu ko sako na jajantwa al’umma da gwamnatin Sakkwato ta fitar game da lamarin da ya faru Ungushi, muna kira ga gwamnati da su ji tsoron Allah su tuna alkawalin da suka dauka na kare al’umma da dukiyoyinsu, an talautar da mutane an kashe su, noma ya buwaya, yakamata a mayar da hankali kan matsakar tsaon da ake ciki.”
Mutanen Ungushi sun tafi karamar hukumar Jega a jihar Kebbi in da suke gudun hijira a makarantar Furamare ta Nizammiya.
Alhaji Sa’idu Atta Ungushi tsohon Kansila a Mazabar Ungushi ya ce sun tafi Jega ne domin tana kusa da su, neman agaji.
“Muna koke shin wane laifi ne muka yi wa gwamnati da za ta kyale mu ana kashinmu, da idona na ga jirgi ya zo kuma ya gansu amma ba abin da ya yi masu ya wuce abinsa, barayin sun shigo garinmu da babur sun fi 1000, gwamnati ba tura mana komai ba, an kashe soja hudu, muna rokon gwamnati in laifi muka yi a yafe mu a samar mana wurin zama, an kashe mana mutane sun fi 30, na wuce shekara 40 ban taba rasa sallar Jumu’a ba sai wannan karon, ta taimaka ta korar muna mutanen nan, sun kashe mana mutane sun kona dukiyoyinmu motoci da shaguna da kayan abinci.”
Ya ce mutanen da suke cikin Makarantar da ke gudun hijira suna da yawa sun fi 5000 a kauyukka daban daban kamar Ungushi, Mai ko Guda, Agwada, Birnin Malam, Nasara da Tingarge.
Ya yi kira ga gwamnatin Sakkwato ta taimaka masu, suna cinkin kunci da matsalolin rayuwa kan wannan rashin tsaro.Malama Tunba ta ce gwamnati ta taimake su an kashe masu mazaje da mahaifa diyansu sun bace ba su san in da suke ba, suna gudun hijira a Jega, rayuwarsu tana cikin matsala. “an kashe min dana ina cikin matsala, rayuwar tana wahala a taimaka mana ina kallo aka yanka min babana, ina za mu sa kanmu,” ta fadi tana kuka.
Shugaban sojoji yanki na Takwas (GOC 8 DIVISION) Mejo Janar Bemgha Paul Koughna ya ziyarci garin Keɓɓe a ranar Lahadi da ta gabata bayan harin da ‘yan bindiga suka kawo suka kashe sojoji huɗu da mutane da dama a garin Ungushi don ganewa kansa halin da ake ciki da kuma ɓarnar da aka samu da kuma sanin irin yanda za a sake salo a yaƙin da ake yi da ‘yan bindiga.
Ziyarar ta nuna kamar sojoji za su yaƙi ‘yan bindigar a yankin yadda aka ƙara zuba jami’an sojoji domin ɗaukar matakin hana kai hari a kan iyakar Kebbi da Sakkwato.
A ziyarar GOC ya gana da jagororin al’umma domin sauraren kokensu ya kuma roƙe su da rinƙa bayar da bayani ga jami’an tsaro kan lokaci.
Ya yi kira ga mutane kar su yi ƙasa a guiwa wurin bayar da haɗin kai ga jami’an tsaro.
Gwamnan Sakkwato Alhaji Ahmad Aliyu a wani taro da ya yi a ƙaramar hukumar Boɗinga Gwamnan ya ce “a matsayin mu ‘yan adam mun yi abin da yakamata mu yi, muna kan yi, mun saye kayan aiki, mun saye kayan yaƙi, mun yi duk abin da yakamata mu yi, Allah mun tuba dubarar mu ba ta iyawa, ƙarfinmu bai yi ba mu iya komai, kai ka yi, muna neman gafara, ka kawo mana ƙarshen waɗannan ‘yan ta’addar, Allah ka isar mana gare su,” kalaman Gwamnan Sakkwato kenan.
Waƙilinmu ya tuntuɓi mai baiwa Gwamna shawara kan harkokin tsaro kanal Usman Ahmed mai ritaya kan Mutanen Keɓɓe sun yi ƙorafi kan rashin ɗaukar matakin da yadace a matsalar tsaron yankinsu, ga shi an kashe masu mutane sama da 32 amma ko saƙon jaje ba ku aika masu, balle ku je, mi za ka ce kan haka?
Ya ce “Gwamnatin Sakkwato ta samu labarin baƙinciki da kaɗuwa kan rasa mutane 32 da sojoji huɗu. Mun samu labarin mutane sun yi nasarar kashe ‘yan bindigar Lakurawa su 13 a harin da suka kawo.
“Amadadin Gwamnan Sakkwato muna miƙa saƙon ta’aziyarmu ga dangin margaya da kuma hukumar sojin Nijeriya da duk ƙauyukkan da lamarin ya shafa a jihar Sakkwato. Muna roƙon Allah ya gafarta masu, ya kuma baiwa waɗanda suka samu rauni lafiya.”
Ya ƙara da cewa gwamnati ta ɗauki matakai kamar haka, ta umarci dukan jami’an tsaro su ƙara matsa ƙaimi sai a hukunta waɗannan ɓatagarin. Samar da kayan ɗaukin gaggawa da suka shafi magani da sauran abubuwan rage raɗaɗi a wuraren da abin ya shafa. An yi kwamiti ƙarƙashin mataimakin Gwamna za su ziyarci in da lamarin ya shafa domin jajantawa da kuma gano irin hasarar da aka yi domin gwamnati ta yi abin da take iyawa. Ƙarfafa haɗin kai tsakanin jami’an tsaron jiha da ƙananan hukumomi da jami’an tsaro domin hana faruwar haka a gaba.
“Gwamnatin jiha ta ƙara bayar da tabbacin kare rayuwa da dukiyoyin jama’a, muna kira ga mutane su kwantar da hankali su cigaba da ba da bayanin tsaro a cikin lokaci.
“Haka kuma kan maganar da Mai girma Atiku Abubakar ya yi da sauran masu ruwa da tsaki, gwamnatin jiha tana aiki tuƙuru da Gwamnatin tarayya a ƙara yawan jami’an tsaro domin ganin an kawar da ‘yan bindigar Lakurawa.“






