NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NICE
@wattpad AuntyNice.
SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI
SHAFI NA 45📑
__________📖 Rai a ɓace Ummi ta dubi Hassan tace, “Hassan nace bazaka auri Aisha ba, Aisha ƴa tace babu wanda ya isa ya chanja, ko ita hauwan ce ta matsa saidai mu rabu, don wanda yafita iko da ita ya mallaka mun ita duniya da lahira”.
Duk illahirin jikin Ummi rawa ya keyi, nidai ganin haka sai na razana, don ban taɓa ganin Ummi cikin wannan yanayin ba, saboda hakan da sauri na ƙarasa jikinta, hawaye ne yafara zuba mun ina riƙe da hannunta nace, “Ummi na Aisha ƙanwar muce dukkan mu babu mai aurenta, Aisha ma baza tayi aure yanzu ba sai ta gama karatun ta, ita da kanta zata zaɓi mijin da ta keso Ummina, ki kwantar da hankalinki” na faɗa ina share hawayen idon Ummi.
“Hakane Aisha ta tabbata zata auri mohd kenan, ƙanin Aunty domin Baban Narabi auren ta kawai yake son gani, kuma a irin halaccin da ya maku ya kwar da kanshi akan Aisha, ko na rana ɗaya bai taɓa nuna muku ko sa muku ido akan Asiha ba, ya kamata kuma ku daure ka bashi haɗin kai yaga auren Aisha da ran shi”, Uncle Abdallah ya faɗa idon shi nakan Abba da Ummi.
Girgiza kai Abba yayi alamar maganan Uncle haka yake, sannan ya maida kallon shi kan Ummi yace, “Fatima naso ace kin haƙura da hukuncin Allah kin yarda an sanarwa Aisha cewa bake kika haifeta ba, idan yaso sai a haɗa aurenta da ɗaya daga cikin yaranki, kinga komai yazo mana da sauƙi, tuwo na maina, amma idan kika bari Aisha ta auri wani daban, tou daga ranan ta fita daga ikon mu, kuma ko ba daɗe ko ba jima zatasan bake kka haifeta ba”, Abba ya faɗa da muryan rarrashin Ummi.
Girgiza kai Ummi ta keyi alamar a’a, bata samu daman buɗe bakinta tayi magana ba kawai muka ga Aisha a tsugunee a gefen Ummi, muryan ta cikin rauni tace, “Ummi idan bake kika haife ni ba waye ya haifeni? Ummi kigaya mun wacece ta haifeni bayanke?” tana jijjiga hannun ummi tana kuka.
Runtse idanun ta Ummi tayi da ƙarfi bata furta komai ba, har saida Aisha ta ƙara maimaita tambayanta babu adadi tukun Ummi tace, “Aisha nice nan na haife ki, bakiga kin fi su Hassan kama dani ba? ae nice na haife ki”, ta faɗa tana miƙa hannu wa Aisha da nufin ta matso jikinta, amma sai mukaga Aisha ta miƙe ta tsaya, a hankali ta matsa kusa da Uncle Abdallah, hannu ta miƙa ta riƙo nashi, muryanta na rawa tace.
“Uncle duk duniya babu matar da nake so sama da Ummi na, amma cikin ƙasan zuciyata kuma babu abinda nake so dagani koji irin ka Uncle, kaida Baban Narabi ina jinku a raina fiye da tunanin wani mai tunani, wataran ina tunanin kaman nafi jin sonka sama da iyaye na”, sai kuma tayi shiru tana sheshsheƙan kuka, a hankali ta cigaba da maganan ta.
“Uncle kaine ka haifeni ko? Don Allah uncle kace mun ehh kaine, don wallahi Yayah Hussain duk duniya nake jin zan iya aure na rayu cikin farin ciki da kwanciyar hankali”, ta ƙarasa faɗi tana faɗawa jikin Uncle Abdallah.
Uncle Abdallah ma kukan yake yi bayan ya rungumeta, hala tun rasuwar Baba Umar yana jin bai sake kuka irin na yau ba, hannun ta ya jawo suka zauna, a hankali yafara warware mata komai, tun daga auren iyayenta har haihuwarta, har rasuwar Babanta, har zamanta hannun Ummi.
Tashi Aisha tayi fuskanta da murmushi da hawaye, ƙarasawa tayi jikin Ummi ta rungume ummi, sun daɗe a haka sai Asiha ta ɗago tanata murmushi ta dubi Ummi.
“lallai Ummi na ke ƴar aljannah ce, dubi irin son da kika mun kamar ke kika kawo ni duniya? Lallai Baba Umar yana kwance a kabarin shi hankali kwance don an nunawa gudan jinin shi kulawa, wallahi ban taɓa maraici ba kuma bazan taɓa ba, idan har ke Ummi da Abba kuna raye, kuma bazan taɓa kukan rashin Baba Umar ba, don kuɗin kune shi,” tana murmushi ta sake riƙo hannun Ummi tace, “Ummi na kinsan daɗin da nakeji don naji ba ke kika haifeni ba kuwa”? ta faɗa fuskarta da tsananin fara’a, hakan yasa Ummi ta daina kukanta ta ƙura mata ido cike da mamakin maganan Aishan.
“Aisha akwai wani mummunan abu dana miki ne a riƙon dana miki har kike murnan bani na haife ke ba”? Ummi ta faɗa a razane, tashi Aisha tayi ta tsaya tana duban Aunty Hauwa tace, “Aunty duk duniya babu mai zuciyar imani irinki keda Ummi na, ke kika sadaukar dani gareta don ta samu kwanciyar hankali, ita kuma tayi riƙo da Amana ta riƙe tamkar ita ta haife ni, kuɗin iyayena ku ƴan aljannane, zumunci ku ba kowa zaiyi ba, naji daɗi zan auri Yayah Hussain ɗina, Ummi na ta ko ina zata zama mun uwa, bani da matsalan komai a rayuwata, yau zanje wurin Baban Narabi na rungume shi nace mishi ɗan tsohu mai ran ƙarfe”, ta ƙarasa maganan cike da farin ciki a fuskarta.
“Aisha baki isa ki auri Hussain ba, ni nan ni zaki aura ko kin ƙi ko kinso, saboda ni nake sonki ba Hussain ba”, Hassan ya faɗa yana matsuwa kusa da ita.
Da sauri Aisha ta matsa kusa dani, “Yayah Hussain ka gayawa yayah Hassan kana sona, kagaya mishi yau ya sani, don ni kai kaɗai nakeso a rayuwana, kuma bazan iya son kowa bayan kai ba”, ta faɗa tana riƙo hannuna.
Hannu na saka na janye nata, ina duban ta cikin ido nace, “na taɓa cewa ina sonki? Ni har abada ke ƙanwata ce, amma Hassan shi yana sonki, saboda haka shi zaki aura, ni zan jira Fatima ce ta girma”.
Ihun Aisha ne gaba ɗaya ya firgita kowa da yake parlourn, da guda Aisha ta faɗa jikin Ummi tana cewa, “Ummi ki basu umurni mana Ummi na, kice yayah Hussain shi zai aure ne, dole Yayah Hassan yayi haƙuri, ni ba shi nake so ba”, bata jira me Ummi zata ce ta tashi taje da gudu ta rungume Aunty hauwa, murya da ƙarfi tace, “mamie nah!”.
Runtse ido Aunty hauwa tayi, don Aisha bata taɓa furta mata mamie na ba, kullum Aunty hauwa ta ke ƙiranta, “mamie na kice musu ni yayah Hussain nake so, yayah Hassan yayi haƙuri”, ta faɗa tana ƙanƙame jikin Aunty hauwa.
Duban kowa Hassan ya tsaya yanayi, chan yace, “naga wanda zai aura miki Hissain ɗin bayan ni nake sonki, wallahi saidai kowa ya rasa daga ni har Hussain ɗin, idan yaso a bayar da ke wa ɗan’uwan kin chan kowa ya rasa a nan”, ya faɗa cike da ɓacin rai.
Abba ne ya saka kowa ya nemi wuri ya zauna, haka yayita ƙoƙarin kwantar mana da hankali, nidai na danne duk wani abu da nakeji game da Aisha a zuciyata, domin ina son farin cikin mahaifiyata da ɗan’uwa na, amma narasa mai yasa Hassan ya kasa fahimtar komai, kodan shine ƘADDARAN DA YA RIGA FATA akanmu?
A lokacin Ummi ta nunawa kowa abinda taji tsoro ya faru a tsakanin mu, muryah a raunane tace, “na daɗe da sanin Allah ya saka ƙauna mai girman gaske a zuciyar ƴaƴana akan Aisha, tou su ƴan biyu ne, wa zan zaɓa wa Aisha wa zan bari? Don Allah ku fahimceni, nasan Hussain da irin haƙurin shi, duk irin son da yakeyiwa Aisha zai iya haƙura wa ɗan’uwan shi, amma kuma an shiga hakkin shi, don tun tana baby yake ce mun wannan ne wife ɗina idan muka girma ko? Tou Hassan kuma nasan halin shi ko na rana ɗaya bazai taɓa haƙurawa ɗan’uwan shi ba, kunga kuma Aisha ita hankalinta nakan Hussain ne, ta yayah zaman su da Hassan zai kawo mana farin ciki? Saboda haka nabar muku wuƙa da nama ku warware komai”, sannan ta dawo da kanta kan Aunty hauwa tace.
“Hauwa kinga dalili na tun farko ko? Bawai bana son mu haɗa ƴaƴanmu aure bane, kawai ina son kwanciyar hankalin Aisha ne fiye da komai, don idan ba tare da Hussain ba bazata taɓa samun nutsuwa ba, shi kuma Hassan ba zai taɓa bamu haɗin kai ba”, Ummi ta faɗa tana share hawayenta.
Murmushi Uncle Abdallah yayi sannan ya gyara zaman shi yana fuskantar kowa, “tou ae ina ganin daga Hassan har Hussain mu muka haife su, basu suka haife mu ba, inaga tou babu wanda yafi ƙarfin mu a cikin su, yadda Hussain zai iya haƙuri da farin cikin shi don ɗan’uwan shi ya samu, tou me yasa shi Hassan ɗin bazai iya yiba? Ita fa Aisha ta riga da ta raba gardama, ta nuna Hussain shi ta aminta dashi, tou mai zai hana bazamu bata shiba? Shi kuma Hassan sai yaci girma ya haƙura, Allah zai bashi wacce tafi Aishan idan yayi haƙuri”.
“Bazan taɓa haƙura da abinda nake so ba, dole ne ma a bani Aisha ko kuma dukkan mu a hana kowa, amma bazai yiwu dukkan mu ku kuka haife mu ba amma zuciyar ku kullum sai tayita karkata kan ɗaya, don nafi kowa sanin dukkanku kunfi son Hussain akaina, shiyasa kuka nunawa Aisha son shi tun tana ƙarama, dama da niyyyanku akan shi shikaɗai ko”? ya faɗa yana hararan inda nake.
Tsawa Abba ya daka mishi, muryah a hargitse Abba yace, “na rantse da Allah Hassan babu mai baka Aisha, kuma idan ni na haife ku gobe zamu tafi wurin Baban Narabi a ɗaura auren Hussain da Aisha, domin mu muka haife ka bakai ka haife mu ba, kuma Hussain yafi dattaku da kamala, yafi ka chanchanta da auren Aisha, idan ya maka zafi ka gyara halinka, saboda haka kowa ya tashi ya bani wuri, kuma ku kwana da shirin tafiya Narabi gobe idan Allah ya kaimu da rai da lafiya”.
Duk parlourn babu wanda bai razana da ɓacin ran da Abba ya shiga ba, domin shi mutum ne mai haƙuri da kawaici, daga gani Hassan ya kure shi ne, shiyasa yayi wannan masifan, ganin haka kowa ya tashi yabar musu parlourn, kowa jiki a sanyaye, na miƙe zan tafi Abba yace, “Hussain kaida Abdallah ku tsaya.”
Duk jikina rawa yake yi, ina tsugune dai-dai ƙafan Ummi, chan naji muryan Abba yana faɗin, “Hussain nasan kai mai haƙuri ne da ƙoƙarin nuna kulawa akan damuwan naka, wanda Hassan yakasa koyi da halinka, kuma a jikina inajin ko bayan raina kaine zaka tsaya mun akan gidan nan, Hussain na baka auren ƴata Aisha, ina son ka riƙe ta da amana tsakanin ka da Allah, kuma bana son kayi gaba da Hassan, don nasan tabbasa sai ya nuna maka, amma kaja girmanka, kuma ku kula da kwanciyar hankalin mahaifiyar ku don bata da Lafiya kada a ɗaga mata hankali da fitina kaji? Jeka Allah yayi muku Albarka”.
Ummi hannu ta saka tana shafa kaina, amma bata iya cewa komai ba, sai hawayen dana lura yana ta bin fuskanta, kiss na mata a forehead ɗinta sannan na miƙe na bar su a parlourn.
Da asuba na tashi na shiga toilet nayi wanka nayi alwala na fito nayi raka’atul fajir, na miƙe zan fita zuwa mosque domin yin sallan asuba, kawai wani irin mummunan ihun Ummi na naji har cikin ƙwaƙwalwar kaina, da gudu na fita nayi hanyar side ɗin Ummi, ina zuwa daidai parlourn ta naga Aunty hauwa ma da Uncle Abdallah da Daddy da sauri sun ƙaraso bakin ƙofan ɗakin Aisha, inda a kasan wurin muka ga Ummi ta faɗi kaman wata gawa, da sauri Abba yayi kanta shida Aunty hauwa, ni kuma nida Uncle Abdallah muka leƙa ɗakin Aisha da yake ƙofan a buɗe.
Wani mummunar faɗuwar gaba naji wanda tunda na zo duniya ban taɓa ji ba, wani irin jirine naji yana shirin kaini ƙasa, badon komai ba sai don ganin Aisha ƙanwata, rabin raina kwance gaba ɗaya jini na malalae a jikinta, ban tashi fahimtan komai ba kawai naji ni na zuɓe ƙasa, babu abinda na kara ji sai ihun Aunty hauwa itama tana faɗowa kaina”.
Dr Hussain yana kawowa nan ya sunkuyar da kanshi yana zubar da hawaye mai masifan yawan gaske, duk illahirin jikin shi rawa yake, yana wani kuka ko mace albarka, murya a bayyane yana cewa, “shikenan Aishan mu, Allah sarki Aishan mu”.
Hummy ganin yanayin da Dr ya shiga ya sakata tafiya inda yake da sauri ta rungume kanshi tana kuka tace, “Mutuwa tayi? Aishan dama ta mutune baby? Wayyo baby na kayi shiru don Allah, ina su Ummi”? Ta faɗa tana ƙara rungume shi a jikinta, shi kuma baiƙi ba ya manna kan shi a ƙirjinta yana kuka mai sautin gaske.
Gaba ɗaya su Abbi kukan suke shi da su Ummi, faisal ma kuka ya keyi kaman mace, Amaal kuma zuwa tayi ta rungume Ummi tana nata kukan.
Jijjiga kai Daddy yake tayi yana faɗin “wannan shine ikon Allah, wannan duniya ƙaramar wurine, ikon Allah humaira wani ƙaddaran ne yake shirin maimaita kanshi kuma, yau kuma mai nake sake ji da gani a rayuwata?” yana kuka ya ƙarasa wurin Dr Hussain ya ɗaga shi daga jikin Hummy, duban irin yadda idon Dr ya koma ya saka shi jawo jikin shi ya rungume shi ƙam a jikinshi yana kuka yana bubbuga bayan Dr.
Ni Aunty nice juyawa nayi na dubi miss xerks da ta wangale baki tana shaftara kuka kaman ance mata yau za’ a mata auren dole da Hassan nace, “besty zo mu koma nigeria muyi kukan sai mudawo gobe idan Allah ya kaimu muji me yake faruwa ne? Hala ma mum sayyeed da jikar kulu suna ta vibration don suji me yake wakana, haka muka fita sum- sum- sum mu ka bar su suna kukan su.
©AUNTY NICE CE✍🏻✍🏻✍🏻




