Home Siyasa ‘Yan Gwagwarmaya za su kafa ƙungiyar Tinubu Must Go

‘Yan Gwagwarmaya za su kafa ƙungiyar Tinubu Must Go

3
0

Wasu ’yan gwagwarmaya sun kafa gangamin Tinubu Must Go domin wayar da kan ’yan Najeriya kan burinsu na ganin an kawo ƙarshen mulkin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta hanyar zaɓen 2027.

Daya daga cikin jagororin gangamin, kuma lauya mai zaman kansa, Barr. Hamza Nuhu Dantani, ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da Arewa Updates.

Dantani ya ce, sun kafa gangamin ne saboda ba su gamsu da yadda gwamnatin Tinubu ke tafiya ba, yana mai iƙirarin cewa daga cikin alkawuran da shugaban ƙasar ya yi bai aiwatar da ko kaso biyar cikin 100 ba.

Ya kuma bayyana cire tallafin man fetur a matsayin ɗaya daga cikin dalilan kafa gangamin, yana mai cewar hakan ya jefa miliyoyin ƴan Najeriya cikin mawuyacin hali.

Ya ce, Tinubu Must Go gangami ne na wayar da kan jama’a ba ƙungiya mai tsarin shugabanni da muƙamai ba, inda manufarsu ita ce mutum ya wayar da kan wani domin samun goyon bayan jama’a gabanin zaɓen 2027.

Dantani ya kuma zargi gwamnatin Tinubu da yi wa ’yan adawa da masu sukarta bi-ta-da-kulli da kuma ɗaukar matakan da ya ce sun saɓa wa dimokuraɗiyya, yana mai bayar da misali da dakatar da Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara na tsawon wata shida a lokacin dokar ta-ɓaci ta 2025 wanda fadar Shugaban Ƙasa ta ce an ɗauki matakin ne saboda rikicin siyasa da matsalar gudanar da gwamnati a jihar.

Da Arewa Updates ta tambaye shi ɗan takarar da gangamin yake son marawa baya a 2027, Dantani ya ce ba su zaɓi wani ba a yanzu, amma suna fatan jam’iyyun adawa su haɗe domin samar da ɗan takara guda ɗaya da zai fafata da Tinubu.

Shin wane ɗan takara kuke ganin ya dace wannan gangami ya mara wa baya?

Da yawan mutane suna ganin marawa Atiku Abubakar zai fi zama abin da ya dace su yi ganin yanda ƙarfinsa da karɓuwarsa tafi sauran ‘yan takara wannan zaɓen.

Gwamnatin tarayya ta fi mayarda hankali kan Atiku, shi ma Atikun ya mayar da hankalinsa sosai kan tsare-tsaren gwamnati da yake ganin suna da matsala in da yake suka mai ma’ana.

Da yawan manazarta na ganin Atiku zai iya samun nasara a jihohi 15 a Arewa, ya kuma samu nasara a jihohi 7 na Kudu.

Wannan nazari zai sa ƙungiyoyin matuƙar suna son taka rawa mai tasiri tau za su aje duk wani bambance-bambance su mara takarar Atiku.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here