Home Rahoto ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 50 sun sanya haraji a...

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 50 sun sanya haraji a Sokoto

14
0

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da sama da mutum 50 a ƙauyen Garin Idi mahaifar mataimakin Gwamnan Sakkwato Alhaji Idris Muhammad Gobir.

Mutanen garin sun ce maharan sun shiga garin ne a tsakanin ƙarfe 10 na dare zuwa 12:30 a ranar Litinin sun yi harbi kan mai uwa da wabi domin tsorata mutanen ƙauyen daga nan suka rabu gida biyu cikin ƙauye.

Majiyar ta ce kashi na ɗaya na ‘yan bindigar sun shiga cikin gidaje sun kwashi kusan mace 30 sun tafi da su daji.

A cewarsa kashi na biyu da suka tafi wata makarantar Allo sun tafi da maza sama da 20 ƙanana da manyan almajirrai da suke karatu a makarantar, ka ga an tafi da sama da mutum 50 kenan.

Ya ce kafin su bar ƙauyen sun saki mutum ɗaya in da suka aike shi ya tafi ya sanar da mai gari da Liman da sauran jagororin gari su same su domin tattaunawa.

“Bayan mai gari da Liman sun je a tattaunawar ne ‘yan bindigar suka nemi a biya kuɗin fansa miliyan ɗaya ga matan, dubu 600 ga sauran waɗanda aka kama,” a cewarsa.

Ya ce bayan kammala zaman mutanen gari sun zagaya gida-gida ƙarƙashin kulawar mai gari da liman aka haɗa dubu 600 aka hannuntawa ‘yan bindigar, anan take da suka karɓi kuɗin suka saki waɗanda suka riƙe, amma suka ce ba za su saki matan ba sai an kawo miliyan ɗaya kuma a kawo kuɗin cikin kwana biyu.

Ya zargi ‘yan bindigar sun dawo garin ranar Talata 7 na dare sun nemi a biya su harajin dubu 300 ko su yi garkuwa da wasu mutane.

“Mutanen kauyen cikin gaggawa suka haɗa dubu 300 suka miƙa masu. ‘Yan bindigar suna cikin garin tsawon lokaci hakan ya sa dole mutane suka haɗa magriba da Isha kafin lokaci ya wuce,”.

Mutanen gari sun roƙi gwamnati da jami’an tsaro da gaggawa su ƙarfafa jami’an tsaro a yankin, sun koka domin mafi yawan su manoma ne.

DSP Ahmad Rufa’i Mai magana da rundunar ‘yan sandan Sakkwato ya ce ba su da bayani kan lamarin domin ba a cika  kawo masu rahoto daga wurin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here